Babbar manufa kuma abinda aka fiso shi ne mutum ya rika ganin cewar shi mai aikata laifi ne, ba wai ya yi ta kallon wasu suke yin hakan ba, watakila ma shi yasa wasu al’amuran suke ta kara cakudewa maimakon samun gayaran su. Sai kowa ya fara ganin kan sa cewar shi ma wanda yake aikata laifi ne, ya kuma dauki zuwa hanyar gyara ba kawai ya yi ta kallon tamkar mutum daya shi ne matsala ba.
Lokacin da Sarkin Agege yake tattaunawa da ‘yan jarida a ofishinsa wanda yake Agege Lagos yana daya daga dattawan mu na Arewa kuma Iyaye mazauna jihohin yamma, (Alhaji Sani Sha’aibu mai goro) wanda kuma shi ne sardaunan Agege, Legas ya roki’yan Nijeriya da cewar suma su gyara kansu.
Sarkin Agegeya yi kira da cewar mu sai mun samu gyara halayen mu, ba irin al’adarnan da aka saba da ita ba ta zagin Shugabanni, abin kuma da yakamata mu sa a gaba shi ne mu rika yiwa shugabannin mu addu’a, saboda ita ce kadai hanya mafita da kuma gyara halaye. Alhaji Sani Sha’aibu Saudaunar Agege ya kara da cewa kowa alhakin wajen bayar da gudunmawa dangane da shi al’amarin gyaran kasarnan, wannan alhakin kuma ya hau kan manya da kuma yara ba kawai wasu su ware kansu daga baya ba, suna taimakawa ta-addanci wannan ba ita ce mafita ba.
Saboda haka suma fa suna da haki a wannan kasa tamu. Alhaji Sani Sha’aibu Saudaunar Agege daga karshe ya bayyana cewar duk wanda ya ci zalin wani ko kuma yana cutar da shi, Allah zai bi mai hakin sa saboda haka sai mun gyara halayen mu ne Allah zai taimake mu. Allah ya ba Nijeriya da ‘ya’yanta zaman lafiya amin.