Rabiu Ali Indabawa">

’Yan Nijeriya Na Fuskantar Karancin Sinadarin Wanke Hannu – NBS

A ranar Talata ne, hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana yawan ‘yan Nijeriyan da ba su da halin sayen sinadarin wanke hannu a gidajensu.

A ko da yaushe hukumomin lafiya su kan bayar da shawarar yawan wanke hannu domin kauce wa kamuw da cutar Korona. A cikin rahoton hukumar NBS na illolin cutar Korona, wanda ta gudanar a Nijeriya a watan da ya gabata.
Ya nuna cewa, “duk da fadakarwan kariya da a ke yi wa ‘yan Nijeriya, mafi yawancin mutane na fuskantar karancin sabulun wakanke hannu.
“Kasancewa sabulu yana da matukar mahimmanci a cikin kayayyakin da ake amfani da su, mafi yawancin mutane sun tabbatar da cewa su na sayen sabulu ne lokacin da za su yi amfani da su.
“A cikin watan Yuni, kashi 24 na gidaje ba su da halin sayan sabulun wanke hannu, yayin da kashi bakwai su ka bayyana cewa ba su da ishasshen wanda za su yi amfani da shi wajen wanke hannu.
“Talakawa suna fama da rashin samun damar sayan sabulun wanke hannu da kuma karancin ruwan wanke hannu.”
Rahoton ya bayyana cewa, mafi yawancin gidaje suna fuskantar karancin ruwan shi da kuma ruwan wanke hannu sakamakon rashin samun damar samun ruwan. Rahoton ya kara nuna cewa, mafi yawancin gidaje ba sa iya sayan ruwa, yayin da kashi 17 su ke fama da rashin ruwan da za su sha, sannan kashi 28 suna fana da rashin ruwan da za su wanke hannu da shi. Magidanta wadanda su ka kai kashi 79 sun bayar da rahoton cewa, suna fama da rashin iya sayan sabulun wanke hannu.
Hukumar NBS ta bayyana cewa, a duk wata cutar Korona tana yi wa gidaje guda 1,950 illa a bangaren tattalin arziki da sauran abubuwan more rayuwa. Ta ci gaba da cewa, an fara kaddamar da wannan bincike ne a watan Afrilun shekarar 2020 tare da hadin gwiwar bankin Duniya.

Exit mobile version