‘Yan Nijeriya Na Kashe Dala Biliyan 5 A Kan Janareto Duk Shekara – Dogara

Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Hon Yakubu Dogara, ya ce, akalla dala biliyan biyar  ne ‘yan Nijeriya ke kashewa a kan janareto a ko wace shekara.

Dogara, ya ce, gwamnatin tarayya na kokari tare da ‘yan majalisar dari bisa dari ta yadda za a kawo karshen matsalar da ke fuskantar wutar lantarki a kasar.

Kakakin majalisar ya kara da cewa, ba za su amince akan yadda ‘yan Nijeriya ke  kashe dala biliyan biyar a kan janareto a kowace shekara ba.

Dogara, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, a birnin Abuja wurin wani taron hulda da jama’a wanda kwamitin majalisar wakilai kan makamashi ta shirya.

Exit mobile version