‘Yan Nijeriya Na Neman INEC Ta Ba Su Ƙarin Rumfunan Zaɓe 9,777 – Farfesa Yakubu

Hukumar Zabe

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa ya zuwa ranar 15 ga Fabrairu, hukumar ta karɓi buƙatun da ba ta nema ba har guda 9,777 daga sassan ƙasar nan na ƙarin rumfunan zaɓe.
Ya lura da cewa waɗannan buƙatu da aka kawo, waɗanda guda 5,700 ne a Oktoba 2020, sun ƙaru da sama da 4,000 a cikin watanni huɗu kacal.
Yakubu ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci ofishin Ƙungiyar Tuntuɓa ta Mutanen Arewa (ACF) a Kaduna ranar Talata domin tattaunawa kan batun ƙarin rumfunan zaɓe a ƙasar nan.
Shugaban hukumar ya ce dalilin ziyarar tasa shi ne domin ya gana da shugabannin ƙungiyar ta ACF saboda ya yi masu bayani kan tsarin da hukumar ta ke da shi na ƙara yawan rumfunan zaɓe a ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa batun da ake yi na ƙarancin rumfunan zaɓe babbar matsala ce da ta shafi ƙasa baki ɗaya.
Ya ce: “Tun a cikin 1996 mu ke da rumfunan zaɓe guda 119,973, amma yawan su bai canza ba saboda tun a 1996 aka yi ƙiyasin cewa za su iya ɗaukar masu zaɓe da aka yi wa rajista mutum miliyan 50.
”A cikin 1999, ƙasar nan ta na da masu zaɓe da aka yi wa rajista mutum miliyan 84 amma kuma yawan rumfunan zaɓen bai sauya ba.”
Ya yi nuni da cewa a dalilin haka, ana samun ɗimbin cinkoso kuma hakan ya na matuƙar ƙuntata wa masu zaɓe a ranar zaɓe.
Yakubu ya ce hukumar ta na so ta ja hankalin kowa da kowa don a inganta tsarin dimokuraɗiyya.
Ya bayyana cewa an fara bin hanyar da za a gyara lamarin tun a makon jiya lokacin da hukumar ta yi zaman tattaunawa da jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyi, hukumomin tsaro da kuma kafafen yaɗa labarai.
Ya ƙara da cewa tuntuɓar juna wani muhimmin abu ne a kowace dimokuraɗiyya, kuma hakan ne ya sa hukumar ta ga ya dace ta yi tuntuɓa, saboda ta samu ra’ayoyin ‘yan Nijeriya daga ko wane lungu da saƙo.
A cewar sa, hukumar ta na faɗaɗa tattaunawar da ta ke yi zuwa ƙungiyoyin zamantakewa da al’adu, da na gargajiya da na addini, da hukumomin gwamnati irin su Majalisar Tarayya da Cibiyar Zartaswa ta Tarayya (FEC) da Cibiyar Gudanar da Ƙasa.
Ya ce hukumar ta tuntuɓi dukkan ƙungiyoyi a sassan ƙasar nan kuma har wasu sun fara turo da saƙonni ta hanyar tes.
A lokacin da ya ke maida jawabi, Sakatare-Janar na ACF, Alhaji Murtala Aliyu, wanda shi ne ya tarbi shugaban na INEC da tawagar sa, ya bayyana jin daɗi da ziyarar, ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da goyon bayan duk wani shiri da za a kawo da nufin inganta rayuwar jama’a da kuma ƙasar baki ɗayan ta.
Ya ce, “Tun a cikin 1996 ba a ƙara yawan rumfunan zaɓe ba. Mu na ganin ya dace a ƙara yawan su don a sauƙaƙa wa tsarin dimokuraɗiyya.”
A cewar sa, “Ɗaya daga cikin matakan wucin gadi da aka ɗauka shi ne ƙirƙirar wasu rumfunan zaɓe waɗanda aka liƙa da manyan rumfuna, kuma hakan ya samu karɓuwa a wurare da dama. Saboda haka abin da ake buƙata shi ne a maida su rumfuna masu cin gashin kan su.”
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya masu kishi
da su ilmantar da jama’a kan batun faɗaɗa rumfunan zaɓe saboda a tabbatar da ɗorewar su.

Exit mobile version