Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 33 a Nijeriya na fama da matsananciyar yunwa, inda ya buƙaci gaggawar ɗaukar mataki daga gwamnati.
Akpabio, ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya buɗe zaman majalisar bayan hutun da ta je, inda ya jajanta wa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a jihohin Bayelsa, Sakkwato, Zamfara da wasu jihohi.
- Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
- Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Ya ce rashin tsaro, tsadar rayuwa da matsalar wutar lantarki suna ƙara wahalar da rayuwar ‘yan kasa.
“Ba da magana ake maganin yunwa ba. Ana buƙatar manufofi, kasafin kuɗi da aiki na gaskiya,” in ji shi.
Akpabio ya buƙaci ‘yan majalisa da su mayar da hankali wajen inganta aikin noma, hanyoyin karkara, ban ruwa da amfani da injina domin yaƙi da ƙarancin abinci.
Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.
Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.