Bello Hamza" />

’Yan Nijeriya Sun Kai Mutum Miliyan 198 –NPC

Hukumar kidaya ta kasa “The National Population Commission (NPC)” ta bayyana cewa, a halin yanzu yawan ‘yan Nijeriya ya kai mutum Miliyan 198, yawan mutanen dake zaune a birane kuwa ya karu da kashi 6.5.

Shugaban hukumar NPC, Mista Eze Duruiheoma, ne ya sanar da haka a garin New York ta kasar Amurka a lokacin da yake gabatar da jawabi tare da nuna matsayar Nijeriya a taron kasa da kasa karo na 51 a kan nazarin manyan birane da zirga-zirgan dan adam da kuma hijirar jama’a daga kauyuka zuwa manyan birane na duniya wadda hukumar “Commission on Population and Debelopment” ta dauki nauyi gabatarwa.

Duruiheoma ya ce, “Nijeriya tana nan a matsayinta na kasar da ta fi yawan mutane a Afrika tana kuma na bakwai a yawan mutane a duk duniya da mutum Miliyan 198.

“Bincike da masana suka yi ya nuna cewa nan da shekarar 2050 Nijeriya zata zama kasa na 3 a yawan mutane a duniya”

“A shekaru 50 da suka wuce yawan jama’ar dake zaune a manyan biranen Nijeriya yana karuwa da kashi 6.5 a duk shekara ba tare da karuwar ababen more rayuwa dai-dai da karuwar jama’ar ba”

“Yawan jama’armu ya karu daga kashi 17.3 a shekarar 1967 zuwa kashi 49.4 a shekarar 2017. Haka kuma rahoton day a yi nazari a kan manyan birane na shekarar 2014 “World Urbanisation Prospects report” ya yi hasashen cewar nan da shekarar 2050, kashi 70 na ‘yan Nijeriya za a same su ne manyan biranen kasar nan”

“Bincike da nazarin yawan mutanen kasar nan na shekarar 2010 ya nuna cewa kashi 23 na daukacin jama’ar kasar nan da ka tattauna dasu mata ne ba maza ba”

Ya ce, yawancin mutane da aka samu a biranenmu matasa ne masu kananan shekaru, musamman kuma matan da suke cikin ganiyar iya haihuwa da wadanda suke da jini a jika, ma’ana wadanda suke da karfin yin aiyuka.

Ya kara da cewa, yawan jama’ar dake shigo wa da kuma yawan masu gudun hijira na cikin gida hakan kuma yana kawo matsala ga ingancin tafiyar da biranen ta yadda ba za a ji dadin rayuwa a biranen ba, ma’ana za a yi rayuwa a cikin kunci a biranen.

“Nazari da bin diddigin wadanda aka tarwatsa “Displacement Tracking Matrid round DDI” da aka gudana a watan Janairu na shekarar 2018 ya nuna cewar, kusan mutum Miliyan 1.7 na zau ne a sansanin ‘yan gudun hijira na fiye da iyalai 321,580 a jhohi 6 na yankin Arewa maso gabas kashi 40 na mutanen kuma na zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijira yayin da mutum Miliyan 1.4 suka dawo gidajensu domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu.

“Yawan ‘yan gudun hijiran ya karu da kashi 4.5 in aka kwatanta da mutum 1,702,680 da Round DD ta gano watan Disamba na shekarar 2017.”

Duruiheoma ya ce, kamar dai na sauran kasashe masu tasowa, birane a Nijeriya na fama da matukar talauci da rashin aikin yi har na kashi 18.4, kamar dai yadda rahoton Hukumar Kididdiga ta kasa (NBC) na shekarar 2017 ya bayyana.

Shugaban hukumar kidaya ta kasa ya nuna tsananin takaicinsa a kan rashin tsaro da karancin harkar kiwon lafiya ga matasanmu da mata masu shekarun haihuwa.

“Nijeriya na kokarin ganin ta yi maganin matsalar ‘yan tawaye a Arewa maso Gabas abin daya kara yawan ‘yan gudun hijira na cikin gida da ake fuskanta a Nijeriya.

“Mu na sane da cewa mata da yara kanana musamman ‘yan mata ne suka fi fadawa cikin rikici in an samu matsalar gudun hijira, saboda haka ne muke mayar da hankalinmu a kansu domin basu kulawa na musamman”

“Muna shirye domin tabbata da mun basu cikkaken kulawa domin a rage mace-mace mata a lokuttan haihuwa da gyara makarantun da suka lallace da kuma karfafa mata ta hanyar basu jarin gudanar da sana’o’i. Bama son mu bar wani a baya wajen cimma burnsa na rayuwa”

Duruiheoma ya ce, wadannan kalubalen suna matukar kawo cikas ga irin rayuwar da jama’a ke gudanarwa a biranenmu. Ya kara da cewa, Nijeriya na nan a kan bakanta na cimma muradun karni na “Habitat Agenda” sanar da matsugunai da kuma samar da tsarin zaunar da mutane a birane a daidai lokacin da duniya gaba daya ke zama wata birni na musamman.

Duruiheoma ya sanar da haka a wata takardar sanarwar da raba wa manema labarai ranar Talata. Ya ce, hukunta wadannan ‘yan sanda zai dawo da mutuncin ‘yansanda a idon ‘yan Nijeriya.

 

Exit mobile version