Wasu ‘yan Nijeriya sun bukaci a kara fadakawar da ake yi akan barnar da cutar kanjamau ta ke yi a cikin al’umma.
Wadanda kamfanin dillancin labarai (NAN) ta tattaunawa da su, sun bayyana cewa, tun da aka samu barkewar cutar korona sai aka kawar da kai a kan wasu cuttukar da ke fuskantar al’ummar Nijeriya, ciki kuwa har da cutar kanjamau.
A nasa tsokanci, wani mai suna Mr Damilola Akintunji, mai shakara 41 a duniya wanda kuma yake zaune a unguwar Lekki ta jihar Legas, ya jinjina wa gwamnati da wasu kungiyoyi akan yadda suke kokarin yaki da cutar a cikin shekarun da suka wuce.
Akintunji ya kuma kara da cewa, “Muna godiya, a halin yanzu muna da cibiyoyin bayar da magunguna cutar kanjamau a fadin kasar nan.
“Amma dai muna bukatar karun fadakarwa don al’umma su fahinci yadda za su kare kansu daga cutar.”
Ana sa tsokacin, wani dan kasuwa, mai suna Mr Emmanuel Afiawari, ya ce, cutar kanjamau ba bakon cuta bane a cikin Nijeriya, sai dai wasu har yanzu ba su yarda da cutar ba, akan haka yakamata a kara kaimi wajen fadakar da al’umma kan cewa lallai cutar kanjamau gaskiya ne.
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 1 ga watan Disamba a msatayin ranar kanjamau ta duniya.
Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Murabus Din Sakatarenshi
Daga Khalid Idris Doya, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad...