Muhammad Awwal Umar" />

’Yan PDP 35,000 Suka Koma APC A Neja

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Shugabannin jam’iyyar APC dubu arba’in ne daga matakin jiha zuwa kananan hukumomi da mazabu suka amincewa shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari da gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello da sake yin takara karo na biyu. Shugaban jam’iyyar APC ta jihar Neja Inijiniya Muhammad Imam ne ya bayyana hakan a bukin karban masu canja sheka su dubu talatin da biyar daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Shugaban yaci gaba da cewar duba da irin kwazon shugaban kasa da gwamnan jiha akan tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar nan da suka kokarta akwai bukatar ba su dama dan dawo wa karo na biyu. Dan haka wannan na nuna cewar jama’a sun gamsu da jagorancin wadannan limaman canjin, mu a matakin jam’iyya muna goyon bayan abinda jama’a suka amince da shi dari bisa dari.

Da ta ke karban masu canja shekar, shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa, Fatima Tijjani, ta yabawa tunanin wadannan ‘yan siyasar na dawo wa APC dan ci gaba da yaki da rashawa da kokarin farfado da tattalin arzikin kasa da maigirma shugaban kasa ya sanya a gaba.

Tsoffin kwamishinoni da tsoffin shugabannin ma’aikatar gidan gwamnati da tsoffin masu bada shawara ga gwamnatin da ta gaba ne bisa jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Aminu Yusuf ne suka canja shekar. Da yake bayani ga gangamin APC da suka karbe su, tsohon mataimakin shugaban PDP din na jiha, Alhaji Aminu Yusuf yace sun canja shekar ne kwazo da jajircewar maigirma shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello saboda irin gudunmawar da gwamnatinsu ta bayar na farfado da tattalin arzikin kasa da lalubo hanyoyin da za a samu zaman lafiya a kasar nan. Dan haka akwai bukatar ‘yan Najeriya da jihar Neja da su amince da sake tsayar da su takara karo na biyu.

Da yake karin haske, wani dattijo kuma jigo a jam’iyyar APC a jihar Neja, Alhaji Hamza Yanga Buba, yace lallai karban wadannan baki da jam’iyyar APC tayi a jihar Neja, abin a yaba ne. Domin sun zo a lokacin da kasar nan ke bukatar hadin kan al’umma ta yadda za a iya lalubo hanyar da ciyar da kasar nan gaba.

Sai dai dattijo ya jawo hankalin masu canja shekar da su shaida har a zukatansu cewar sun dawo ne dan samun hadin kai da ci gaban jihar nan, jama’a su sani idan jam’iyyar siyasa ta lalace mutane ne suka lalata ta, haka idan tayi kyau jama’ar ne suka kyautata.

Shugaba makaho ne yana bukatar ‘yan jagora na kwarai kusa da shi, dan haka da mu da wadanda suka shigo yanzu da mu tabbatar mun zama fitila ta alheri ga wannan tafiyar.

Mu sani halin da kasar nan ke ciki tana bukatar jajirtaccen mutum mai tsoron Allah kamar shugaba Buhari, domin kowa ya shaida irin namijin kokarin da yayi na ganin ya dora kasar nan a wannan yanayin da ta ke akai yanzu, a matakin tarayya kowa shaida ne akan ayyukan shugaba Buhari, idan ka duba a matakin jiha ma maigirma gwamna ya zama wanda ya cima burinsa a sauwake, domin ayyukan da ya sanya a gaba ya samu nasara akan su ba tare da farfaganda ba, mun yaba kuma mun gamsu sosai.

Da yake karin haske, shugaban kungiyar tallata manufofin shugaba Buhari a jihar Neja, Alhaji Isah Sidi Rijau, ya yabawa da dawo war wadannan bakin, ya ci gaba da cewar wannan taron na gangamin karban masu canja sheka Buhari Campaing Organisation aka yiwa ba APC ba, domin yadda jama’a suka gamsu da kudurin shugaba Buhari akan kasar, wanda hakan na nuna cewar zai iya cin zabe a 2019 ba tare da fargaba ba.

Yanzu haka muna shirin yin gangamin lumana na mutane miliyan daya akan nuna goyon baya da tursasa shugaban kasa kan ya sake amincewa da takara karo na biyu a jihar nan, dukkanin wadanda suka dawo mutane ne masu natija da kima wadanda kuma sun san sirrin siyasa, ya zama wajibi mu sanya kishi, mu hada hannu wajen kawo ci gaba a kasar nan.

 

Exit mobile version