Connect with us

LABARAI

’Yan PDP 400 Sun Koma APC A Jihar Ekiti

Published

on

Fiye da ‘yan jam’iyyar PDP 400 karkashin kungiyar “Prince Adedayo Adeyeye Mobement (PAAM),” dake karamar hukumar Irepodun/Ifelodun ta jihar Ekiti suka canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Wadanda suka canza shekan sun fito ne daga garuruwan Eyio da Esure da Iropora na karamar hukumar. Mista Ayodele Matthew ne ya jagoranci wadanda suka canza shekan daga bangaren Esure-Ekiti yayin da Mista Adeyeye Ajibola ya jagoramci wadanda suka fito daga bangaren Iropora.
Tsohon mai bai wa gwamna Ayodele fayoshe shawara a kan siyasa Ademola Bello, shi ne ya karbi sabbin wadanda suka canza shekan ya kuma bukaci su saki jikinsu domin jam’iyyar APC bata bandance tsakanin tsoho da sabon dan jam’iyyar wajen adalci.
Ya kara da cewa, dan takarar gwamna na jam’iyyar Dakta Kayode Fayemi, mutum ne mai mutumci wanda a kullum burinsa shi ne fitar da jama’a daga kangin talauci.
Daga nan ya bukaci sabbin ‘yan jam’iyyar dasu koma mazabarsu su kuma yi aiki tukuru wajennganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben gwamna dake tafe a ranar 14 ga watan Yuli. Mista Ayodele da Ajibola da kuma Ogunsakin sun bayyana cewa, sun bar jam’iyyar PDP ne saboda ya mayar da jam’iyyar kamar wani kayan gidansa yana juya ta yadda ya ga dama.
Sun kuma kara da cewa, shugabansu Prince Dayo Adeyeye, mutum ne mai mutumci suna kuma da tabbacin zai taimaka wajen samun nasarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, sun ce tuni suka gane cewa, Fayose ya mayar da duk wani dan jam’iyyarb APDP kamar bawa gare shi.
Advertisement

labarai