Connect with us

LABARAI

’Yan Sabuwar PDP Za Su Sanar Da Matsayarsu A Wannan Makon – Baraje

Published

on

A kwai bayanan dake nuna cewar za a ci gaba da tattaunawar da ake yi tsakanin jam’iyyar APC da sabuwar jami’iyyar PDP a wannan makon da muke ciki.
Wannan yana zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban sabuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Kawu Baraje, ya ce, mambobin jam’iyyar za su bayyana matsayinsu na yadda zasu ci gaba da tafiyar da harkokin siyasar su a cikin wannan makon da muke ciki.
Majiyarmu ya shaida mana cewa, an ci gaba da tattauna wa yadda za a ci gaba zama a cikin jam’iyyar APC tun lokacin da aka kammala babban taron jam’iyyar APC na kasa.
Wani babban dan jam’iyyar APC wanda ya nemi mu sakaya sunansa ya ce, zuwa yanzu an kusan kammala tatauna dukkan abubuwan da suka kamata na yarjejeniya tsakanin sabuwar jam’iyyar PDP da kuma jam’iyyar APC.
“Mun kammala hadaddaiyar babban taron jam’iyyarmu ta kasa inda aka yi taron tare da dukkan shugabanin dukkan bangarrorin, an kuma girmama dukkan wanda ya kamata a girmama.
“Ba a karbe musu mukamansu na kwamitin zartarwar jam’iyyar ba, ina tunanin abin daya kamata mu ci gaba da tunani shi ne yadda zamu karfafa jam’iyyarmu domin fuskantar zaben dake gaba.”
Tuni dai bangaren sabuwa jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Alhaji Baraje ta bayyana aniyarta na sanar da matakin da zata dauka a wanna makon da muke ciki. A ranar Lahadi ne aka fitar da sanarwar a babban ofishin yakin zaben Kawu Baraje dake garin Ilori.
Ya ce, ana sa ran a cikin makon ne zasu kammala tattauna dukkan abin daya dace na matakin daya kamata su dauka.
Baraje ya kuma kara da cewa dukkan jadawalin bukatunsu, kamar dai yadda suka mika wa shugabannin jam’iyyar APC na nan kuma zasu bayyana wa jama’a a nan gaba.
Ya ce, dukkan bukatunsu don ci gaban Nijeriya ne ba wai don kashin kansu ne ba.
“Mun dade muna tataunawa tsakaninmu kuma yanzun lokaci ya yi da zamu sanar wa ‘ya Nijeriya matsayinmu, musammam ‘yan Nijeriya masu mana fatan alhairi.
“Babban bukatun ‘yan Nijeriya da kuma samar da hadaddiyar Nijeriya ne babban burinmu, ba kasar da ake danne masu rauni ba.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: