‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-13 Sun Kammala Zagaye Na Farko Na Aikinsu A Wajen Kumbo

Daga CRI Hausa,

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, ta ce ’yan sama jannati na kasar Sin Zhai Zhigang da Wang Yaping, sun kammala aikinsu na farko a wajen kumbo, inda suka koma cikin kumbon Tianhe.

Hukumar ta ce wannan aiki shi ne irinsa karo na 3 da aka yi yayin da ake gina cibiyar sararin samaniya ta kasar, kuma irinsa na farko da ’yan sama jannati na Shenzhou 13 suka yi. Haka zalika, shi ne aikin ’yan sama jannati na farko a wajen kumbo da ya kunshi mace a tarihin kasar Sin, tana mai ayyana aikin a matsayin nasara.

Mutanen biyu sun koma kumbonsu ne da mislain karfe 1:16 na dare agogon Beijing, bayan sun shafe saoi 6 da rabi suna aiki. Haka kuma sun kammala jerin ayyukan da ya kamata su yi.

Yayin aikin nasu, an yi gwajin sabbin rigunan zamani na tafiya a wajen kumbo da kasar Sin ta samar da muamala tsakanin ’yan sama jannati da masu aikin kula da naurori da kuma gwajin inganci da amincin kayayyakin dake da alaka da aiki a wajen kumbo.

A ranar 16 ga watan Oktoba ne kasar Sin ta kaddamar da Shenzhou-13, inda ta tura ’yan sama jannati 3 da za su yi aikin tsawon watanni shida wajen gina cibiyarta na sararin samaniya. (Faiza Mustapha)

Exit mobile version