Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda A Borno Sun Dakile Yunkurin Sace Wani Karamin Yaro

Published

on

Rundunar yan-sanda a jihar Borno ta bayyana dakile yunkurin sace wani karamin yaro, dan kimanin shekara 8-Ibrahim Ahmed, wanda shima da ne ga shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Askira Uba, Alhaji Ibrahim Muhammed da ke jihar.

Kwamishinan yan-sandan jihar Borno, Mista  Demian Chukwu, ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai, birnin  Maiduguri.

Chukwu ya ce, bisa ga bayanai da suka samu daga iyayen yaron, al’amarin ya faru ne a ranar Jumu’a, inda wasu da ba a san ko su waye ba a suka je takanas har makarantar firamaren da yaron yake karatu, inda suka yi awon gaba dashi zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Ya kara da cewa, bisa ga wannan ne rundunar yan-sandan ta dauki matakin gaggawa wajen baza jami’an tsaro masu yaki da yan fashi da makamai tare da wasu jami’an tsaro na musamman- domin gudanar da samame a lungu da sako, wanda daga bisani aka ceto yaron.

“Nan take na bayar da umurnin datse hanyoyin fita daga garin, tare da gudanar da binciken kwakwaf ga duk wata motar da ke kokarin fita daga garin”.

“Ta dalilin wannan ne ya taimaka wadanda suka sace yaron suka rasa wurin gudu, shi ne sai suka gudu suka bar yaron a cikin mota tsawon awanni 5. Wanda daga bisani muka ceto yaron tare da mika shi ga iyalan sa”.

“Kuma har yanzu muna kan aikin neman masu laifin domin samun damar kama su”.

Bisa ga samun yawaitar garkuwa da mutane a jihar, kwamishinan yan-sanda Mista Chukwu ya gargadi shugabanin makarantu da cewa su rika lura da mutanen da ke zuwa suna daukar yan makarantar.

Ya ce, ga shi yanzu kasa ga mako guda an samu matsalar satar mutane har aji biyu a babban birnin jihar Borno.

“Wanda idan baku manta ba, ko a ranar 19 ga watan Satumba, saida wasu bata-gari suka sace karamin yaro dan shekara 4- dan shugaban jam’iyyar APC a jihar Borno, Alhaji Bukar Dalori, kuma an sace yaron ne a makaranta, duk da a cikin taimakon Allah, jami’an mu na FSARS suka gano shi”.

“Bugu da kari, muna nanata yin kira ga yan siyasa da jama’ar a jihar Borno baki daya, kan su rinka waiwayen bayan su tare da kai rahoton kowacce barazana ga jami’an tsaron da ke kusa dasu”. Inji shi.

 
Advertisement

labarai