Daga Rabiu Ali Indabawa,
A ranar Laraba Rundunar ‘yan sanda a Jihar Filato ta fitar da sanarwar fara farautar wasu ‘yan bindiga da suka kashe mutane hudu a Bassa dake Jihar Filato.
Rundunar ta yi alkawarin kamawa tare da hukunta wadanda suka yi kisan. Mista Edward Egbuka, kwamishinan ‘yan sanda (CP) a jihar, ya ba da wannan bayanin lokacin da ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Talata a Jos.
Kwamishina ‘yan sandan ya tabbatar da kisan mutane hudu a kauyukan Rikwe-Chongu da Zirshe na Miango Chiefdom a Karamar Hukumar Bassa. A cewar Egbuka, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma. Ya ce har yanzu ba a kama mutane ba. Amma, ya ba da tabbacin cewa ana ci gaba da bincike kuma nan ba da dadewa ba za a cafke wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
Kwamishinan, wanda ya ce zaman lafiya ya dawo cikin jihar, ya nuna rashin jin dadinsa cewa an hargitse a cikin makonni shida da suka gabata tare da yawan kai hare-hare a Karamar Hukumar Bassa. “A da ana samun zaman lafiya a Filato, amma an samu matsala a cikin makonni shida da suka gabata. “Duk abin da muke yi shi ne mu tsaurara matakan tsaro kan lamarin tare da tabbatar da an samar da dawwamammen zaman lafiya cikin jihar.
A taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Litinin, Kwamishinan ya ce an yi shi ne domin nemo mafita mai dorewa ga ci gaba da samun tarnakin rashin tsaro a wasu sassan jihar. A nata bangaren, kungiyar Ci gaban Irigwe (IDA) ta yi Allah wadai da mummunan lamarin, tare da bayyana shi a matsayin “abin bakin ciki.”
A wata sanarwa da Sakataren yada labarai na kasa na IDA, Mista Dabidson Malison ya fitar, ya nuna rashin jin dadinsa tare da yin kira ga hukuma da ta kamo wadanda suka aikata kisan tare da sanya su fuskantar fushin doka. “Shugabancin na IDA ya yi bakin ciki, da nuna damuwa da ci gaba da faruwar wannan danyen aikin ba wai kawai ya nuna mugunta da shedanci ba ne har ma da rashin mutuntaka ga dan’Adam a kan mutanen Rigwe,” in ji shi.
Ya kuma ce: “An yi cikakken adalci don kawo karshen duk wata barna ta rayuka da dukiyoyi a kasarmu.”