Jami’an ‘yan sanda na farin kaya FSARS dake jihar Kano sun samu nasarar kwato mota kirar Mercedes Benz ML350 a titin Hadeja dake cikin jihar da wasu gungun ‘yan fashi da makami da suka fito daga yankin Masaka dake cikin jihar Nasarawa. Sunci nasarar ce bayan sunbi sawu, sun kuma cafke wadanda ake zargin ne a cikin wata mota kirar Sports Utility a cikin jihar.
Kakakin rundinar yansandan jihar, SP Magaji Majiya ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar talatar data gabata. Wadanda aka cafke su hudu sune, Kenneth Adam, Ali Jafaru, Abdulkadir Shaka da Aliyu Audu, wadanda dukkan su sun fito ne daga yankin Masaka dake Nasarawa da kuma wadznda suka fito daga yankin Gunduwawa Kuarters dake cikin jihar Kano.
Majiya ya ce, gungun sun kai hari ne a wani gida a Masaka a ranar 22 ga watan Satumbar 2018 suka sace motar kirar Mercedes Benz ML350 mai dauke da lambar Abuja , ABC 554AY da wasu kaya masu tsada.Rindinar ta kuma kwato tabar wiwi a Tudun Wazirchi da a anguwar Badawa dake Kano, inda a yawanta ya kai 189 aka kuma kiyasta kucinta ya kai naira miliyan 6. 6.
A cewarsa, a ranar 19 ga watan Satumba da kimanin karfe 1500 wani one Musbahu Usman da a ka fi sani da Dangaja dake anguwar Kofar Na’isa da wani Nura Hussain, da a ka fi sani da Lado dake anguwar Jambulo a Kano sun hada baki suka yi wa wani da yaje banki don ya dauko kudinsa naira 500,000 fashi sun kuma kai wa wani farmaki a kan titin Audu Bako dake Kano a lokacin da zai hau a daidaita sahu suka kwace lasa kudinsa har ya samu raunuka an kwato kudin kuma ana kan yin bincike an kuma gano sun juma suna aikata irin wannan ta’asar.