’Yan Sanda Sun Bazama Farautar Wasu Sufetocin Bogi Masu Damfara A Abuja

Shanu

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta fadakar da mazauna yankin kan ayyukan ‘yan damfara, wadanda ake zargin suna zagayawa don karbar kudi daga masu shirya taro da sauran mazauna garin da sunan masu aiwatar da yarjejeniyar Korona. Yayin da yake karyata jita-jitar da ke yawo na cewa mambobin rundunarsa na da hannu a aikata laifin, FCTA ta ce rundunar ‘yan sanda ta FCT ta fara farautar kungiyar masu aikata laifin.

Shugaban, Kafafen yada labarai da wayar da kai na rundunar tsaro ta FCT Korona, Kwamared Ikharo Attah, wanda ya tabbatar da ana aikata wadannan munanan rahotanni, ya gargadi jama’a da su yi hankali da irin wadannan masu aikata laifukan da ke bayyana kansu a matsayin wakilan gwamnati. Ya kuma jaddada cewa, tawagar ta Shugaban kasa a kan Korona ko kuma FCTA ba ta ba kowa izinin hukunta masu karya ka’idojin kiwon lafiyar ba.

Attah ya kara da cewa kotunan tafi-da-gidanka da gwamnati ta kafa ne kawai ke da ikon hukunta masu karya doka. Ya shawarci mazauna yankin cewa duk gungun mutanen da aka samu suna karbar kudi daga hannun jama’a ta kowace fuska ya kamata a sanar da su ga hukumomin da suka dace, yana mai jaddada cewa irin wadannan ayyukan sun ci gaba da zama haramtattu.

Kalaman nasa sun bayyana kamar haka: “A zahiri muna aiki ne a kan tsari na gaskiya, kasancewar Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya kafa tare a karkashin shugabancin Kwamishinan ‘Yan sanda na Babban Birnin Tarayya, Bala Ciroma, ba ma fita neman kudi a wurin mutane a kan batutuwan da suka shafi jagororin Korona.

“A zahiri muna guje wa haduwa da mutane don neman su ba mu kudi a kan kowane abu. Amma abin takaici ne da damuwa matuka a ce muna jin irin wadannan jita-jita, cewa mutanenmu suna zagayawa da sunan tilastawa Korona. “Ba mu da wani ofishi ko wani mutum daga jami’in dubawa na Korona, wanda muka ba shi damar yin zagaye kan wannan aiki. Kwamishinan ‘yan sanda, wanda shi ne shugabanmu, bai yarda da irin wadannan jami’an da za su zagaya ba. Duk wadanda ke cikin wannan aikin ya kamata su guji hakan. PTF a matakin kasa sun bamu dokoki da ka’idoji na jagoranci da ladabi domin mu kiyaye.

“Akwai abubuwan da suka ba da izini su yi aiki a cikinsu da suka hada da bude makarantu, amma kawai su suna bi ne suna ƙuntatawa mutane a kan wasu abubuwa da mutane ya kamata su yi.”

Exit mobile version