‘Yan Sanda Sun Cafke Lauyan Bogi A Jihar Jihar Osun

Rundunar ‘yan sandar Jihar Osun ta cafke wani mutum mai suna Yekini Ajao, bisa yunkurin amsar kudade daga hannun mutane, inda yake daukar hankalin mutane a kan cewa shi lauya ne. Majiyarmu ta labarta mana cewa, an kai kusan makwonni da dama ana farautar sa. Majiyarmu ta kara bayyana mana cewa, an samu nasarar cafke Ajao ne lokacin da yake gudanar da ciniki da wasu mutane masu bukatar taimakon lauya a Osogbo. An dai gurfanar da wanda ake zargi a kotun Jihar Osun, wacce take da zama a Osogbo ranar Juma’a, ya aikata wannan laifi ne a ranar uku ga watan Afrilun shekarar 2019.
Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kasa Elijah Oluwasegun, ya bayyana cewa wanda ake tuhuma yana bayyana kansa a matsayin lauya, inda yake damfarar mutane. Ya kara da cewa, ‘yan sanda ne suka samu nasarar cafke Ajao, bayan da suka dauki tsawan lokuta suna barautar sa.
Wanda ake tuhuma ya musanta laifin da ke tuhumar sa da shi.
Alkali mai shari’a Segun Ayilara, ya bai wa ‘yan sanda umurni a kan su ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har zuwa lokacin da aka kammala binciken shari’ar sa. Ayilara ya dage sauraran wannan kara har sai ranar 24 ga watan Afrilu.

Exit mobile version