’Yan Sanda Sun Cafke Magoya Bayan PRP 22 A Bauchi

Jam’iyyar adawa ta PRP a jihar Bauchi, ta yi zargin cewar jami’an tsaron ‘yan sanda a jihar sun cafke mata magoya baya hadi da garkamesu, inda jam’iyyar ta zargin ‘yan sandan da kokarin firgita mata magoya baya da neman sanyaya wa jam’iyyar guiwar kan muradinta na samun rinjaye a kujerun siyasa da dama.
Shugaban jam’iyyar PRP reshen karamar hukumar Bauchi, Sulaiman Musa ya shaida cewar wannan kamen da ‘yan sanda suka yi wa magoya bayansu a daren ranar Alhamis a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida, ya shaida cewar lamarin ya biyo bayan zagayen yakin neman zabe da suka gudanar ta karshe a ranar Alhamis din ne.
A cewarsa, sun zagaya cikin jihar Bauchi ba tare da tayar da hankali kowa ba, “Dukkanin yakin neman zaben da muka gudanar cikin lunguna a sakunan jihar Bauchi mun yi ne a bisa yadda doka ta tanadar, mun kuma kammala a daidai lokacin da aka umurta.
“Amma abun mamaki abun takaici akwai abubuwan da suke faruwa wadanda kamar ana son a fusata ‘ya’yan jam’iyyar PRP. Misali, (Ranar Alhamis) PRP ta yi gangamin karshe na yakin neman zabenta, mun bi hanyoyi da daman gaske a cikin garin Bauchi cikin kyakkyawar yanayi,” Yana mai fadin hakan.
Ya kara da cewa, “Bayan mun kammala sai muka samu labarin jami’an tsaro na ‘yan sanda sun kai farmaki gidan Dowakin dan takarar kujerar majalisar tarayyarmu (Gidan Doki), inda su ka shiga har cikin wannan gidan suka kama mai gadin gidan, masu kula da dawakan gidan, da kuma cafke limamin da ke jagorantar sallah a wannan gidan. Abun bai takaita haka ba, jami’an tsaron sun sake zuwa Sakatariyarmu suka kai farmaki wa mutane, sannan sun yi ta bi suna cafke mambobin jam’iyyarmu,” A cewarshi
Ya shaida cewar babu wani laifin da suka aikata, inda yake shaida cewar sun bincika babu wani laifin da suka yi, kana ya kuma kara da cewa yanzu haka suna masu kira ga shugaban ‘yan sanda na kasa da ya tsawatar wa jami’an tsaronsa da su daina takura wa jam’iyyun adawa a jihar.
Sulaiman Musa ya shaida cewar kawo yanzu mutane 22 ne aka cafke musu. Ya nemi a kawo karshen wannan matsalar domin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, “Dukkanin ‘ya’yan jam’iyar PRP mutane masu son zaman lafiya da son ci gaban kasa,” Inji shugaban PRP.
Shi ma kuma da yake karin haske kan wannan batun, dan takarar kujerar majalisar dattawa da ke neman wakiltar mazabar cikin Bauchi a karkashin jam’iyyar, Alhaji Shehu Abdullahi ya bayyana cewar rade-radin da ake cewa har da shi aka kama a cikin kamen karya ne, ya kuma shaida cewar dumbin farin jini da kuma tulin magoya bayan da yake da sune suka tsokale wa gwamnatin APC ido don haka ne ya yi zargin an shirya musu tubgu ne kawai.
A ta bakin mai neman majalisar, “ni dai babu wanda ya kama ni, abun da na sani shine a ranar, (Alhamis) mun rufe gangamin yakin neman zabenmu wanda muka zagaya cikin kwaryar Bauchi cikin kwanciyar hankali. Mun kammala gangaminmu wajen karfe biyar na yammaci, na yi jawabi wa jama’anmu da cewar a yi zabe lafiya, amma na nemi kowa ya zabi cancanta ya kuma kasa-ya-tsare-ya-raka ya kuma jira sakamakon zabensa.
“Daga baya sai nake samun labarin wai jami’an tsaro sun je gidan Doki na karkashin jagorancin wani dan sanda wai Baba Yola suka cafke mana magoya baya da ma’aikatan cikin gidan, a waje ma sun kara cafke wasu mutane, mutane 22 aka kama mana, amma ni wadanda suka shafe ne mutane 4 ne, sun balla gidan suka shiga ba tare da izini ba,” A cewar shi.
Wakilin Birni ya nuna rashin kwarin guiwarsa kan adalci daga wajen ‘yan sanda, “Ina hasashen gwamnati mai ci za ta iya amfani da jami’an tsaro wajen mana barazana. Don haka muna kira ga hukumar da ke kula da ‘yan sanda da ta tabbatar da sanya ido kan jami’anta,” In ji shi.
‘Yan jarida sun nemi rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi domin jin ta bakinsu, inda Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da cewar sun kame mambobin jam’iyyar guda 22 a bisa zarginsu da tayar da hankulan jama’an jihar, “Abun da ya faru mun samu labari a ranar Alhamis cewar wasu matasa ‘yan barandan siyasa suna tayar da fitina daga yankin Wunti zuwa Jahun, daga nan mun bi su daga nan aka samu matasa a wani gida da ake cewa gidan Doki mun kama matasa 22 dauke da sanduna da sauran makamai, a yanzu haka suna hanun jami’anmu na CID ana kan gudanar da bincike a kansu daga bisa za mu kaisu kotu,” in ji DSP.
Datti ya karyata zargin cewar ana yunkurin yin amfani da jami’ansu wajen daukan bangare a tsakanin jam’iyyu ko ‘yan takara, sai dai ya tabbatar da cewar ba za su taba zura ido wasu na kawo rudani wa zaman lafiya a jihar ba.

Exit mobile version