Idris Aliyu Daudawa" />

‘Yan sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane Bakwai A Kebbi 

‘Yan sanda a  jihar Kebbi sun yi nasarar kama ‘yan kungioyar masu garkuwa da mutane, da kuma aikata sauran laifuka su bakwai, a sassa daban daban na jihar. Kwamishinan ‘yansanda na jihar Ibrahim Kabiru shi ne wanda ya bayyana hakan lokacin daya gana da manema  labarai a hedikwatar rundunar  ‘yansandan da ke Birnin Kebbi babban birnin jihar ranar Alhamis.

Ya bada sunayen  mutanen da aka kama wadanda suka hada da Bello Garba  wanda aka fi sani da suna kwamanda , sai Alti Alh. Chede, Muhammadu da Ali Dutse, sai  kuma Garba Madugu, Umaru Alhaji Magaji, da Aliyu Dikko Dankwarra, sai kuma na karshe Bello Dan Jariri.

Kamar dai kwamishinan ‘tyansandsan ya bayyana su dai wadanda ake zargi da aikata laifukan, an kama su ne, a wurare daban daban na  jihar, an kuma kama su ne da muggan makamai da suka hada da bindigogi da kuma adduna,  hakan kuma ya sa su ‘yansanda suka sa kai hari bayan sun kama su kuma, suka ceto wadanda suka yi garkuwa dasu.

“Su dai  suna dauke da adduna da kuma bindigogi sun kamo mutanan ne ranar 2 ga  watan Oktoba na wannan shekara ta 2018, su kuma wadanda aka ceton tuni aka hada su da iyalansu”.

Kwamishinan ‘yansanda ya bada labarin kama mutane shida wadanda suka shahara wajen satar yayoyi sun shiga ukun sune kuwa, bayan da suka shiga wani shago a cikin garin Argungu inda suka saci  wayoyi (58) wadanda kira daban daban ne wadanda kuma aka yi ma kudi Naira 720,000 sai kuma wasu wayoyi 21 da kuma mashin wanda aka saya da kudaden da aka samu lokacin da aka sayar da satattun wayoyi.

Da yake gabatar da wadanda suka aikta laifin ga manema labarai, har ila yau shi kwamishinan ‘yansandan, akwai mutane biyu wadanda ake zarginsu da yi ma wni mutumi mai suna Usman Umaru a karamar hukumar Bagudo, saboda sun yi ma mutum fashi da makami na mashin ma suna Honda.

Ya kara bayyana cewar dukkan wadanda ake zargi da aikata laifin musamman ma wadanda suke garkuwa da mutane, suna yin ko dai daya daga cikin laifuka ko kuma duka.

Ya yi kira ga mutane a cikin jihar da cewar su ci gaba da ba ‘yansanda hadin kai “Saboda yaki da mutanen da suke aikata ayyukan ba alhakin wata hukuma daya ba ne”.

Exit mobile version