Wani abun rashin imani da rashin tausayi ya sake faruwa a jihar Bauchi inda wani matashi mai shekara 22 mai suna Musa Hamza ke fuskantar zargin hallaka wani karamin yaro mai shekara 17 (Adamu Ibrahim) tare da kasheshi da karfin tsiya, bayan kasheshin ya fille masa kai tare da kwakwale masa dukkanin Idano a karamar hukumar Alkaleri.
DSP Ahmed Mohammed Wakil, Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi shi ne ya shaida hakan ta cikin sanarwar da ta fitar a jiya, ya na mai cewa tunin ‘yan sanda suka kame wanda suke zargi da aikata wannan danyen aikin tare da tuhumarsa bisa kisan kai da aikin ta’addanci.
Sanarwar ta nuna kisan a matsayin na gilla sosai bisa nuna rashin imani tsantsa wajen aiwatar da kisan da kwakwale idanon karamin yaron, da zimmar yin Tsafi kamar yadda matashin ya shaida da kansa.
Sanarwar ta yi bayanin yadda lamarin ya faru daki-daki kamar haka: “A ranar 21 ga watan Disamban 2020, Jami’an ‘yan sandan caji ofis din Alkaleri sun kame wani mai suna Musa Hamza dan shekara 22 da ke kauyen Unguwar Wake, wanda ya yaudari wani mai suna Adamu Ibrahim dan shekara 17 da suke zaune a kauye guda, zuwa bayan garin kauyen tare da hallaka shi da sanda.
DSP Wakil ya shaida cewar dukkanin sassan jikin mutum din sun kwasa zuwa babban asibitin Alkaleri domin nazarin likitoci wanda Likita ya tabbatar da cewar gawar ta mace.
“A yayin bincike, an samo Idanun gawar guda biyu daga hannun wanda ake zargi,”
DSP ya kuma shaida cewar wanda ake zargin da kansa ya amsa laifinsa wanda ya shaida a yayin tambayoyin ‘yan sanda cewar ya aikata hakan ne bisa umarnin da Boka wanda ya nemi ya kawo idanun mutum za a masa Tsafin da zai zama mai arziki.
Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewar daga cikin ababen da suka suka kama a hannun matashin sun hada da Wuka guda daya, na’urar ririta kida (MP3), Laya guda daya da kuma takalmin roba.
Jami’in Yada Labarai na ’yan sandan ya shaida cewar suna kan bincike kuma za su gurfanar wanda suke zargin a gaban kotu domin fuskantar tuhume-tuhume bisa laifin da ya aikata.
LEADERSHIP A YAU dai ta nakalto cewa, wannan lamarin ya faru ne ‘yan kwanaki bayan da jama’an jihar suke cigaba da alhenin da tur da wani lamarin da ya faru na Yanke ma wata karamar yarinya ‘yar shekara shida Al’autarta a karamar hukumar Jama’are wanda wani matashi ya aikata, wanda shi ma bincike ya nuna cewa tsafi yake son yi da Al’aurar na yarinya.