Khalid Idris Doya" />

‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Dan Kasuwa A Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da take zargi da hada hanu wajen kashe wani dan kasuwa mai suna Abba Aminu.

Da yake bayani a lokacin da ya gurfanar da wadanda suke zargin, Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya ya shaida cewar an tsinci gangan jikin mamacin ‘Abba Aminu’ a kusa da wani ginin da ba kammala gina wa ba da ke unguwar Dambare da ke cikin jihar Kano a ranar 20 ga watan Yulin 2018.

Magaji ya kara da cewa; “Iyalan marigayin sun bayar da rahoton cewar sun rasa makusancin nasu ne bayan da ya amshi kiran waya daga wani abokin kasuwancinsa mai suna Sagiru Lawan, inda shi Sagiru ya kira shi da daddare domin ya nuna masa wata filin sayarwa.

“Tawagar masu bincikenmu sun kama wadanda muke zargin da kashe marigayi Abba,” A cewar Kakakin

Ya kara da cewa, wadanda suke zargi Sagiru Lawan da ke zaune a unguwar Goron Dutse ya bayyana da bakinsa kan cewar ya aikata laifin ta’addanci, inda ya kara da cewa wani dan uwansa mai suna Naziru Lawan (wanda yanzu haka suke kai farautarsa), inda ya nemi su tsara kisan tun shekaru biyu da suka wuce.

Wanda ake zargin ya ce; “Dan uwa ya sanyani don na nemo mutanen da za su kashe Abba, sannan ya ba ni naira N150,000 domin na biya su ladan aikinsu. Na amsa kuma na ba su naira N130,000,” A cewar shi

Majiya ya kuma shaida cewar bincikensu ya kai ga gano musu cewar shi ‘Naziru Lawan’ ya bai wa wani mai suna Balele aikin, inda shi kuma ya amsa hadi da gayyatar wani abokinsa mai suna Kabiru Yusuf da aka fi sani da (Alaramma) da ke zaune a yankin Gwarzo domin gudanar da aikin.SP Majiya ya kuma shaida cewar shi ‘Kabiru Yusuf’ yanzu haka sun cafko shi, inda ya kuma bayyana da bakinsa kan cewar su hudu ne suka yi aikin hallaka marigarin.

Majiya ya shaida cewar nan gaba kadan za su gurfanar da wadanda suka cafke din a gaban kotun domin fuskantar shari’a daidai da laifukansu da suka aikita, yana mai kara da cewa za su tabbatar an cafko sauran wadanda suke da hanu domin wazar da adalci.

Exit mobile version