Yusuf Shuaibu" />

‘Yan Sanda Sun Cafke Mutum 323 Bisa Laifin Da Suka Shafi Zaben 2019

Shugaban rundunar ‘yan sandar Nijeriya Mohammed Adamu, ya bayyana cewa an cafke mutum 323, bisa laifin da suka shafi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya na ranar 23 ga watan Fabrairu. Ya kuma bayyana cewa, an kashe ‘yan sanda guda biyu, yayin da aka raunata wasu da dama. Shugaban ‘yan sandar ya yi wannan bayani ne wajen taro bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya wanda ya gudana ranar Litinin a garin Abuja, taron ya hada da kwamishinonin ‘yan sanda da kuma manyan jami’an ‘yan sanda. Shugaban ‘yan sandar ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa za su gurfanar da wadannan masu laifi zaben a gaban kuliya.
Ya kara da cewa, sashin rundunar ‘yan sanda masu binciken laifukan zabe wanda kwamishinan shari’a yake jagoranta tare da hadin gwiwar hukumar zabe, sun kammala binciken laifukan zabe tare da tattara hujjoji.
Adamu ya ce, “Kiddigar wadanda suka aikata laifuka a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a duka bangarorin kasar nan sun kai 323, kuma an samu sanarar cafke su. ‘Yan sanda guda biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama sun samu raunika.” Shugaban ‘yan sandar ya ce, ya bai wa rundunar ‘yan sanda wadanda suka gudanar da aikin zabe umurnin su hada kai da hukumar zabe wajen binciken laifukan tare da gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya. “Sashin rundunar ‘yan sanda masu binciken laifukan zabe wanda kwamishinan shari’a yake jagoranta tare da hadin gwiwar hukumar zabe sun kammala binciken laifukan zaben, inda suka bi kowace Jiha suka tattaro hujjoji, hukamar zabe za ta shigar da kara,” in ji shugaban ‘yan sanda.
Adamu ya bayyana cewa, rundunarsa ta shirya tsaf wajen kokarin tabbatar da ganin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar Jiha ya gudana cikin kwanciyar hankali da numana, ya gargadi ‘yan siyasa da kuma sauran masu shirin tarwatsa.
A halin yanzu dai, kungiyoyi masu sa-ido a kan zabe, sun yi kira da a yi wa dokar zabe garanbawul, inda suka bukaci a daure duk wanda ya kawo rikici a lokacin zabe tare da wadanda suke daukar nauyin su daurin shekara 30 a gidan yari.
Shugaban kungiyar TIFPI, Libingstone Wechie, ya yi kira ga jami’an tsaro su mayar da hankali wajen tsare rayukan mutane da dukiyoyinsu lokacin da ake gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar Jiha ranar 9 ga watan Maris, inda hakan zai bai wa masu jefa kuri’a natsuwa lokacin gudanar da zaben. Da yake bayyana wa manema labarai rahotan kungiyar a kan zaben da aka kammala ranar Litinin a garin Abuja, Wechie ya bayyana cewa, “Shugaban kasa ya karfafa dokar zabe a kasar nan baki daya, ta yadda jami’an tsaro za su tsare kasar daga rikin bayan zabe a duk sassan kasar nan.”

Exit mobile version