‘Yan Sanda Sun Cafke Shugabannin Al’umma Bisa Kashe Barawo

’Yan Fashi

Daga Khalid Idris Doya

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Legas, CP Hakeem Odumosun, ya yi gargadi dangane da masu daukar doka a hannu na hukunta wadanda ake zargi da aikata laifuka a jihar.
Shugaban ‘yan sandan ya sha alwashin dakatar da irin wannan danyen aikin wanda ya ce ya zama ruwan dare.
Don tabbatar da dakile irin wannan, ‘yan sanda a jihar ta Legas a kwanakin baya sun cafke wasu shugabannin al’umma uku bisa zarginsu da illata wani barawo a yankin Ikotun da har hakan ya jawo ajalin ransa.
Kakakin Rundunar a jihar, CSP Muyiwa Adejobi, ya shaida cewa ‘yan sandan da ke aiki a caji ofis din Ikotun sun kama wasu shugabannin al’umma uku a Ikotun bisa zarginsu da ladaka na jaki ga wani barayo.
Ya shaida cewar wanda ake zargi da satar, ya shiga dakin wata mace mai suna Misis Adeyemi Opeyemi a gida mai lamba 2 Asalu Bus Stop, da ked aura da Abaraje Road a Ikotun inda ya yi kokarin mata sata.
A cewarsa, matar ta yi kurururwar neman dauki yayin da barayon ya arci na kare da neman tsarewa daga unguwar lamarin da ya kaisa fadawa hannun wasu ‘yan unguwar da suka ladaka masa na jaki da har hakan ya yi asalinsa.
Adejobi ya shaida cewa shugabannin al’umman da suka kama kan wannan batun sun kunshi Sakariyau Biliaminu mai shekara 66; John Adeyemi mai shekara 77 da kuma Gabriel Ajayi dan shekara 55.
Ya ce, wadanda suka Kaman suna kan fuskantar tambayoyi yadda aka yi har aka kashe wanda ake zargi.

Exit mobile version