Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, Mista Umar Muri ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan jihar ta cafke mutum 29, da ake zargin masu satar mutane ne, da wasu 43, wadanda suka aikata laifuka daban-daban daga ranar 31 ga Oktoba zuwa 31 ga Disamba.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Kaduna a shekaranjiya Alhamis.
Kwamishinan, ya danganta nasarar da kwazon jami’an ‘yan sanda.
Saboda haka, sai ya ci gaba da cewa, yayin da aka kama mutum 29, da yin garkuwa, sauran 53 kuma an kama su ne da ‘yan fashi da makami ko fyade da sata.