’Yan Sanda Sun Cafke Wasu ‘Yan Fashi Biyu A  Ogun

Mazauna Ekiti

Daga Rabiu Ali Indabawa

Tawagar rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Ogun sun cafke wasu mambobin kungiyar ‘yan fashi da makami a yayin da suke gudanar da wani aikinsu na fashi.

Wadanda ake zargin, Olaitan Olushola, wanda aka fi sani da Toshiba; da Oluwajuwon Balogun, an kamasu ne a  yayin da ake zargin su da tsoratar da mazauna Ogijo a yankin Karamar Hukumar Sagamu ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin. Oyeyemi ya ce an kama Olushola da Balogun a lokacin da suka gudanar da fashi.

Ya kara da cewa an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan kiran gaggawa da hedkwatar reshen Ogijo ta samu cewa, mambobin kungiyar suna fashi a yankin Malatori na Ogijo. PPRO din ya ce, “Su (wadanda ake zargin) suna kwace wa mazauna kayayyakinsu ta hanyar nuna musu bindiga.

“A lokacin da aka kira wayar, DPO, Ogijo Dibision, CSP Muhammed Baba, ya hanzarta jagorantar mutanensa zuwa wajen, inda aka kame su biyun, yayin da wasu suka tsere da wasu makamansu. An gano daga cikin mambobin kungiyar biyu da aka yi amfani da su wajen amfani da bindiga.

“Biyu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, Idowu Kareem da Akinloye Raimi, sun bayyana cewa su biyun suna daga wadanda mambobin kungiyar ‘yan fashin suka kwace musu wayoyinsu ta hanyar tsorata su da bindiga.”

Oyeyemi ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Edward Ajogun, ya ba da umarnin a tura wadanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar don gudanar da bincike cikin hikima.

Ya kara da cewa “Kwamishinan ‘yan sandan, ya kuma ba da umarnin a farauto ‘yan kungiyar da suk gudu domin a hukunta su,” in ji shi. ,,

 

Exit mobile version