Yusuf Shuaibu" />

‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Kungiyar Asiri Guda 50 A Jihar Ebonyi

Laifin

A ranar Talata ne, rundunar ‘yan sandar Jihar Ebonyi ta tabbatar da cafke mutum 50 wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne wadanda su addabi jihar. Bayanin sun bayyana cewa, an yi wannan kame ne bayan samun korafe-korafen ayyukan ‘yan kungiyar asiri a yankuna daban-daban na jihar, musammam ma yankunan, Ohaozara, Ohaukwu, Ezza ta kudu, Ezza ta arewa da kuma karamar hukumar Afikpo ta arewa da ke cikin jihar. An bayyana cewa, mutum uku sun rasa rayukansu a yankin Onueke da ke karamar hukumar Ezza da kuma Ezza ta arewa, sakamakon arangamar ‘yan kungiyar asiri wanda ya gudana cikin wannan mako.

Da ya ke tabbatar da Kaman, kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Ebonyi, DSO Lobeth Odah ta bayyana cewa, rundunarta ta na iya bakin kokarin ta wajen dakile ayyukan ‘yan kungiyar asiri a cikin jihar.   

A cewarta, “Jihar Ebonyi ta na da saukin ayyukan ta’addanci a Nijeriya. Amma ayyukan ‘yan kungiyar asiri ya na addabar jihar. Mun cafke  sama da mutum 50 wadanda a ke zargi da gudanar da ayyukan ‘yan kungiyar asiri, da yawa daga cikin sum un gurfanar da su a kotu. “Idan a ka ziyarci gidan yari, za a samu da yawa daga cikin su wadanda a ka yanke musu hukuncin zama a gidan yarin. “Muna bukatar matasa su  canza daga fada wa ayyukan ‘yan kungiyar asiri. Babbar matsalar ita ce, matasa da yawa sun fada cikin  ayyukan ‘yan kungiyar asiri, sannan sun a cigaba da gudanar da ayyukansu a cikin jihar,” in ji ta.

Ta ce, rundunar  ‘yan sanda za ta gurfanar da duk wadanda ta cafke a gaban kotu, domin su fuskanci hukunciu dai-dai da laifin da su ka aikata. Ta kara da cewa, rundunarta  za ta zafafa sintiri a dukkanin yankunan jihar, domin dakile wannan mummunar dabi’a. Ta ce, ‘yan sanda za su kafa rundunar ta musamman domin ayyukan ‘yan kungiyar asiri.

Exit mobile version