Daga Rabiu Ali Indabawa,
’Yan Sanda sun damke ‘yan kungiyar OPC da su ka cafke Iskilu Wakilin Ayete . Ana zargin wadannan mutane da yin kisan-kai a wajen kama wannan mutumi . ‘Yan OPC sun ce Iskilu Wakilin Ayete ne shugaban ‘yan bindigan da ke Ibarapa. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jami’an tsaron sun cafke wadanda su ka kama wannan mutumi da ake zargin cewa ya na garkuwa da mutane.
Ana zargin Iskilu Wakiliin Ayete shi ne shugaban ‘yan bindigan da su ke ta’adi a Ibarapa, Jihar Oyo. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta reshen Jihar Oyo, ta tabbatar da cewa ta cafke mutane uku daga cikin ‘ya ‘yan kungiyar OPC da su ka kama Wakiliin Ayete.
Jami’an ‘yan sandan sun ce an yi wa wadannan mutane tambayoyi a game da kisan kai da su ka yi a wajen yunkurin kama wannan mutumi da ake zargi da laifi. Mai magana da yawun ‘yan sanda na Jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, ya ba da umarnin a wuce da Iskilu Wakiliin Ayete zuwa asibiti.
Jawabin ya ce: “Jami’an ‘yan sanda su na sanar da jama’a cewa da kimanin karfe 9:00 na safe, an kama wasu mutane uku da daga baya aka gana cewa ‘yan OPC ne.” “Sun shiga yankin Kajola, a Ibarapa na jihar (Oyo), da nufin kama wani Bafullatanin mutumi, Wakili, wanda ake zargi da hannu a ta’adin da ake yi wa Yarbawa.”
‘Yan Sanda su ka ce da ‘yan OPC din su ka shiga gidan Wakili, sun banka wuta, hakan ya sa su ka kona wata Baiwar Allah wanda har yanzu ba a gane wacece ita ba.
Jawabin ya karkare da cewa: “A karshe duk wanda ya ke da wani abu da Iskilu Wakili ya kai kara a ofishin CID da ke Iyaganku, Ibadan, domin a gudanar da bincike.”.