Khalid Idris Doya" />

’Yan Sanda Sun Cafke ‘Yar Konar Bakin Wake A Maiduguri

Daga Khalid Idris Doya

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno, a Talatar nan ne take tabbatar da batun  kame wata mace ‘yar konar bakin wake a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bakassi da ke Maiduguri a sa’ilin da take kitsa yadda za ta yi ta tayar da wannan bom din da ta dauko a jikinta.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar, dauke da sanya hanun Kakakin Rundunar Edet Okon, wacce ya rana a Maiduguri,  ya ci gaba da cewa sun samu nasarar kame ‘yar konar bakin waken ne a sa’ilin da take kai-kawo domin ganin yanayin da ya dace don tayar da bam din, ya bayyana cewar ‘yan sandan sun samu nasarar a bisa sa’ayin sashinsu na musamman masu dakile tashi bom wato (EOD) wajajen karfe 6: 50 na safiyar ranar Talatar a sansanin ‘yan gudun hijran.

Jami’in ‘yan sandan ya bayyana cewar rundunar tasu, sun yi kokarin killace muhallin a wannan lokacin, inda ta samu nasarar warwar bom din gami da taso keyar wacce ta dauko bom din. Ya zuwa yanzu kamar yadda ‘yan sandan suka shaida, wacce ake zargin tana gargame a hanunsu.

Okon ta cikin sanarwar nasa ke cewa: “A Talatar nan, wajajen karfe 6:50 na safiya, wata mace wacce take auke da bom, inda ta shiga sansanin ‘yan gudun hijira ta Bakassi (IDP) da ke cikin garin Maiduguri.

“A lokacin da take dauke da bom din, hadakar ‘yan sanda na sashin musamman masu dakile tashin bom, (EOD) sun dauki kakkawar mataki inda inda suka samu nasarar warware bom din daga yunkurin tashinsa,” In ji PPRO.

“Wacce muke zargi mai suna Zara Idriss mun samu nasarar kameta, yanzu haka tana hanunmu a tsare,”

Okon ya bukaci dukkanin jama’a da su ci gaba da gudanar da dukkanin harkokinsu ba tare da wata matsala ba, domin a cewarsa ‘yan sada da hadin guiwar sauran jama’an tsaro suna kan gudanar da dukkanin aiyukan da suka dace domin ci gaba da kare jama’a da dukiyarsu.

Ya sha alwashin cewar a kowani lokaci hakkinsu ne kare dukiya da rayukan ‘yan kasa, don haka za su ci gaba da kawar da bata gari domin wanzar da zaman lafiya a cikin kasa.

Exit mobile version