’Yan sandan yankin da ke Zhenjiang na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin sun samu kiran neman taimako daga wani mutum da ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar fafare cikinsa da wuka a lokacin da ya ga ba zai iya jure zafin ba.
Lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin, sun tarar da mutumin, wanda ake kira Yang, yana numfashi da kyar, kwance cikin jini da wuka a hannunsa tare da wani tufafi da wasu hotuna da suka kewaye shi. Sun sami cikinsa a bude kuma sun dauki matakan agaji na farko don tsayar da zubar jini yayin da suke jiran isowar likitoci.
Wani jami’in ‘yan sanda ya bayyana cewa, “Kwanan nan Yang ya kai mahaifiyarsa asibiti don duba lafiyar ta a Jiangsu’s Suzhou, amma daga baya ta mutu sakamakon mummunan rashin lafiya. Yang ya yi ikirarin cewa ya gata a rayuwarsa bayan mutuwar mahaifiyarsa kuma ya yanke shawarar kashe kansa irin yadda kabilar Japanis suke yi a sheakru dari da suka gabata.
A halin yanzu Yang baya cikin hadari bayan ya samu kulawa a asibitin yankin. Masu amfani da yanar gizo a Sina Weibo na kasar Sin sun masu nuna juyayin ga mutumin. Suna masu cewa, “Mutuwarka ba shi ne abin da mahaifiyarka za ta so gani ba. Tana fatan ka rayu cikin farin ciki kuma rayuwa mai kyau.”