‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 16 Daga ‘Yan Bindiga A Zamfara

Zamfara

Daga Hussaini Yero Gusau,

Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta samu nasarar ceto mutum 16, da aka yi garkuwa da su, a karamar hukumar kaura-namoda da ta Zurmi.

Wadanda aka ceto din sun hada da, mata da kananan yara da aka yi garkuwa da su a kauyen Magarya, mahaifar shugaban majalisar dokokin Jihar Zamfara,Honarabul Nasiru Mu’azu Magarya.

Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ‘yansandan jihar, Ayuba Elkana ya ce, mutum biyar daga cikin wadanda aka sace din sun fito ne daga, kauyen shugaban Majalisar, sannan sauran 11 kuma, ‘yan asalin karamar hukumar kaura-namoda ne.

“An kubutar da su ne bayan matakan da muka dauka tare da goyon bayan gwamna Matawalle na sabon salon yaki da ‘yan bindiga a jihar.

Kwamishinan ya cigaba da cewa, yanzu haka, ‘yan bindida suna fuskantar matsananciyar wahala a jihar, sakamakon matakan tsaro da gwamnatin jihar ta dauka, na kawo karshensu.

Ya ce, “Matakan tsaro da gwamna Matawalle ta dauka, ya sa suke samun sakamako mai kyau, yayin da yanzu ‘yan bindigar ke fada wa cikin mawuyacin hali a jihar”.

Ya cigaba da cewa, ‘yansanda tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, za su cigaba da yaki da ‘yanbindiga, har sai sun kawo karshensu.

A karshe, Kwamishina ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi hakuri kan matakan tsaro tare da cigaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin samun nasarar da ake bukata.

Ya kuma gargadi ‘yanbindigar da ko dai su bar jihar ko kuma su fuskanci mummunan sakamako, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, a kokarinmu na kawar da masu aikata miyagun laifuka a dukkan fadin wannan jiha”.

Exit mobile version