’Yan sanda a Jihar Zamfara sun yi nasarar ceto mutum takwas daga hannun masu garkuwa. ‘Yan sandan tare da hadin gwiwa da tubabbun shugabannin ‘yan bindiga sun kwato bindiga da alburusai. Rundunar ‘yan sandan har wa yau ta yi nasarar kama mutane 22 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da satar mutane, fashi da makami satar kayayyaki fyade da sauran nau’ikan laifuka.
‘Yan sanda sun ceto mutanen takwas daga hannun masu garkuwa a kauyukan Gidan Barga da Dangajeru da ke Kananan hukumomin Tsafe da Talata na jihar yayin da suka kama mutum 22 da ake zargin bata gari ne, The kamar yadda Channels ta ruwaito.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abutu Yaro, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya kira a hedkwatan hukumar da ke Gusau a ranar Lahadi.
Yaro ya yi bayanin cewa ana zargin mutane 22 da aka kama din da wasu laifukan da suka hada da kisan kai da satar mota a sassan jihar.
“Wannan ya faru ne a ranar 15 ga watan Janairun 2021 a yayin da DPO na Shinkafi tare da hadin gwiwar wasu shugabannin tubabbun ‘yan bindiga a garin suka tabbatar da mika AK 47 daya da kunshin alburusai biyu masu harsashi 18.” A cewar kwamishinan, an samu nasarorin ne tun daga 24 ga Disambar 2020 zuwa 14 ga watan Janairu sakamakon jajircewar ‘yan sandan jihar da ke fatattakar ‘yan bindiga.