Daga Rabiu Ali Indabawa
’Yan sanda a jihar Anambra sun gano wata masana’antar sarrafa jarirai da ke aiki a yankin Otolo Nnewi da ke Jihar. Wata sanarwa da Mohammed Haruna, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ya fitar, ta ce an gano masana’antar jarirai wacce ake gudanar da ita a matsayin gidan karuwai yayin gudanar da bincike kan yunkurin yin garkuwa da wani karamin yaro dan shekara hudu da aka yi kwanan nan.
Majiyar LEADERSHIP A YAU ta tunatar cewa a ranar 11 ga Maris, akwai wani rahoto a hedkwatar rundunar da ke Nnewi, cewa wani yaro dan shekara hudu a makarantar St Joseph, Otolo Nnewi, yana dawowa daga Makaranta tare da ‘yan uwansa yayin da wasu maza biyu a kan babur ya kama yaron kuma ya ya tafi da shi. Duk da haka, wasu masu baburan hana sun ceto yaron tare da bin sahun wadanda suka kama a yankin Akamili Nnewi.
Haruna ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin wadanda fusatattun mutane suka bubbuge su an tabbatar da mutuwar daya daga cikinsu, sun ce Gladys Nworie Ikegwuonu ce ta turo su, wacce a yanzu haka suke aiki tare da ita, kuma ita ke kula da masana’antar sarrafa jarirai da gidan karuwai inda take ajiye kananan yara mata. Sannan tana sa a yi musu ciki bayan sun haihu sai ta sayar da jariran ga kwastomomin da ke jira.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya bayar da sunayen mutanen biyu da aka cafke kamar haka; Abuchi Ani, mai shekaru 32, na Ohazora, jihar Ebonyi, da Emeka Ikegwuonu, mai shekaru 49, na Akabukwu, Nnewi, daga Jihar Anambra. Ya kuma bayar da sunayen ‘yan mata hudu masu ciki da aka kubutar da su, kwai; Chisom Okoye, ‘yar shekara 20, daga garin Mgbaneze Isu, yankin karamar Hukumar Onicha, dake Jihar Ebonyi. Sai kuma Chinecherem Clement, ‘yar shekara 18 daga garin Agbaebo Isu a karamara Hukumar Onicha, Jihar Ebonyi. Blessing Ogbonna, ‘yar shekara 21 daga garin Nkwagu Isu karamar Hukumar Onicha, Jihar Ebonyi. Blessing Njoku, mai shekar 21, yar asalin garin Mgbaneze Isu, a karamar Hukumar Onicha, Jihar Ebonyi, dukkan su suna dauke da juna biyu.
Haruna ya kara da cewa rundunar tana kara kaimi wajen cafke babbar shugabar ta su da ake zargi domin gurfanar da ita da sauran wadanda suka aikata laifin gaban kotu.