El-Zaharadeen Umar" />

‘Yan Sanda Sun Cika Hannu Da Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina

Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina ta ce ta yi nasarar damke wasu mutane hudu da suka yi shigar burtu wadanda suka kwarai da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Gambo Isah ya bayyana haka ga maneman labarai a Katsina , ya ce an  samu  nasarar a lokacin da jami’an su suka ga alamun wasu mutane biyu suna yawan shige da fice tare da wani da ya sanya hijabi ya rufe fuskarsa kamar mace.

Ya ce wannan lamari ya faru ne a unguwar G.R.A da ke kusa da ofishin hukumar zabe ta kasa reshen jihar Katsina.

DSP Gambo Isah ya ce sakamakon daukar matakin da jami’ansa suka yi ne ta hanya tura masu sa ido, ya sa suka yi nasarar tsafke mutane hudu da suka hada da Mubarak Babangida dan shekaru 21 da ke unguwar Dutsen safe da Abubakar Lawal Suleiman dan shekaru 19 da ke unguwar Kerau sai kuma Aliyu Lawal dan shekaru 22 da ke unguwar Adoro tare da Nura Abdulhamid da aka fi sani Bazgi dan shekaru 22 duk acikin Katsina.

Ya kara da cewa wadanda aka kama din sun tabbatar da laifin da ake zarginsu da aikatawa inda suka bayyana cewa sun zo domin su sace dan wani mutun kai suna Alhaji Rabi’u Gide mai shekaru hudu Allah bai ba su sa’a ba.

Acewar jami’in hulda da jama’a na rundunar bincike game da wannan lamari dai ya yi nisa saboda haka da zaran sun kammala za su mika su zuwa gaban kuliya manta sabo domin fusknatar hukuncin abinda suka aikata.

A wani labarin kuma jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Gambo Isah ya ce sun kama wani mutun da ake zargin ya kwarai wajan yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

‘Yan sanda sun yi nasarar damke Gambo Lawal mai shekaru 26 dan asalin karamar hukumar Danmusa a ya yin da yake kokarin hada baki da wasu abokansa wanda yanzu ake neman ruwa a jallo domin sace wani mutun mai suna Alhaji Mustapha Kabirn Dogon Gida a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina

A lokacin wannan samamaye an samu layin wayar salula da yawa a hannun wanda ake zargi wanda kuma yake amfani da su wajan aikata laifuffuka kamar yadda bincike ya nuna.

‘’wanda ake zargin bai tsaya baiwa baincike wahala ba, inda ya tabbatar da wannan laifin da ake zarginsa da aikatawa, har ma ya kara da cewa yana cikin mutanan da suka addabi wannan yanki da sace sacen jama’a da kuma fashi da makami’’ in ji shi

 

Exit mobile version