Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke wasu mutum uku bisa wani faifan bidiyo da ke yawo a kafar sadarwa ta zamani, inda aka zagi Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba da ta gabata, ta bayyana cewa cikin wadanda aka kama, akwai wani dattijo mai kimanin shekara 70 a duniya, Lawal Abdullahi Izala, Bahajaje Abu da kuma Hamza Abubakar, wadanda dukkansu suna zaune ne Unguwar Gafai da ke cikin birnin Katsina.
Cikin sanarwar, wacce Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa wasu masu kishin kasa ne suka jawo hankalin rundunar bisa wannan bidiyo da ke yawo, inda aka cusa ma Shugaban kasa da Gwamnan Jihar Kastina zagi, inda wani mai suna Lawal Abdullahi, da ake yi wa lakabi da “IZALA” ya yi zagin.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sanusi Buba ne ya bayar da umurnin a yi bincike kan lamarin, wanda binciken ne ya kai ga wannan kame da aka yi. “Da ake bincikensa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa,” in ji sanarwar.
Wani bincike da muka gudanar ya nuna mana cewa, baya ga shi Lawal Dan Izala, sauran mutum biyun kuma ana zargin daya ne da laifin daukar bidiyon, daya kuma da laifin yadawa.