Yusuf Shuaibu" />

‘Yan Sanda Sun Gano Shanu 61 A Jihar Kaduna

A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandar Jihar Kaduna ta bayyana cewa, ta gano shanu 61 a yankin Kwanar kan babbar hanyar Buruku zuwa Kaduna cikin karamar hukumar Chikum ta Jihar, wanda ake kyautata zagon an sato su ne. Kwamishinan ‘yan sandar Jihar Malam Ahmad Abdurrahaman, shi ya bayyana wa manema labarai hakan a garin Kaduna, inda ya bayyana cewa, a ranar 27 ga watan Fabrairu tawagar ‘yan sanda suka gano shanu ba tare da makiyayi ba, inda suke kyautata zaton an sato su ne.
Ya ce, “Nan take rundunar ‘yan sandar ta fara gudanar da bincike tare da kore shanun zuwa shalkwatan ‘yan sanda da ke Buruku. Saboda haka, rundunar tana sanar da mutane cewa, duk wanda aka sace masa shanu ko kuma suka bace, to ya zo ofishin ‘yan sandar tare da shaidarsa na mallakar shanun domin a ba shi shanunsa.”
Abdurrahaman ya kara da cewa, a ranar 19 ga watan Fabrairu, bataliya na 453, ta sojojin saman Nijeriya da ke Kaduna, ta mika wa runduunar dabbobi guda 57, wanda aka gano a ranar 12 ga watan Fabrairu. Ya ce, dabbobin an kwato su ne daga hannun ‘yan bindiga, dabbobin sun hada da shanu guda 44 da kuma akuyoyi guda 13.
“A cikin dabbobi 57, 17 daga cikin su an mika su ga masu shi guda bakwai wadanda suka nuna shaidar mallakar dabbobin,” in ji shi.
Kwamishinan ‘yan sandar Jihar ya tabbatar wa zauna garin Kaduna cewa, rundunarsa za ta kawar da duk wani laifuka da ake aikitawa a Jihar tare da tsare rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu. “Ya bukaci mazauna Jihar su taimakawa ‘yan sanda da bayanai wajen dakile muyagun laifuka a yankinsu,” in ji Abdurrahaman.

Exit mobile version