‘Yan Sanda Sun Gano Wasu Yara Da Suka Bace Shekaru Biyar Da Suke Wuce A Jihar Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gano wasu yara da suka bace tun a cikin 2014, a shekarar 2014 rundunar ta bayyana bacewar yaran a jihar Legas, wata mata mai suna Christiana Onuchukwu da ake zargin ta sace yaran tana hannun jami’an ‘yan sanda inda suke gudanar da bincike akan ta.

Rundunar ‘yan sanda jihar Legas ta cafke matar mai suna Christiana Onuchukwu da ake zargin ta sace wasu yara biyu da iyayen su ba daya ba, sannan ta rike yaran a hannun ta tun daga shekarar 2014 zuwa yau da aka samu nasarar cafke ta.

Asirin matar ya tono ne a yayin da daya daga cikin yaran mai suna Ikimot ‘yar shekaru 12 ta je wani ofishin ‘yan sanda ta bayyana cewa matar ta sace ta ne wasu shekaru da suka wuce, yarinyar ta na kiran matar da ake zargin sace sun da sunan mama, sannan ta roki jami’an yan sanda su mayar da ita wajen iyayenta na asali.

Dayan yaron kuwa mai suna Ukashatu Musa wanda ake zargin matar ta sace tun yana dan shekaru 6, yanzu yana da shekaru 11 a duniya, yaron ya bayyana cewa kafin matar ta sace shi yana zaune da mahaifiyarsa ne a ungiuwar Ebute-Meta dake jihar Legas, shi Ukashatun da harshen hausa ya yi wa jami’an ‘yan sandan jawabi.

Tuni aka nemu iyayen yaran, inda aka mika musu ‘ya’yansu, sannan an ci gaba da gudanar da bincike kan wacce ake zargin, inda da zarar an kammala binciken za a gurfanar da ita a kotun majestire dake yankin Ebute Meta na jihar Legas din.

Exit mobile version