Khalid Idris Doya" />

‘Yan Sanda Sun Haramta Dukkanin Zanga-Zanga Muddin Babu Izininta A Bauchi

A bisa rikicin siyasa da ake samun aukuwarsu a wasu sassan unguwanni na jihar Bauchi da kuma wasu kulubalen da zanga-zangar masu adawa da kuma maso nuna goyon baya da matakin ayyana zaben gwamnan jihar Bauchi a matsayin wanda bai kammalu ba ke janyo wa jihar, Rundunar ‘yan sandan jihar ta haramta dukkanin wani gangami ko zanga-zanga kowacce iri ce muddin babu amincewa da sahalewa daga rundunar.
Rundunar ta shaida cewar ta dauki wannan matakin ne domin kare rayuka da dukiyar jama’an jihar daga barazanar da wasu gurbatattu ke yi wa zaman lafiyar jihar.
Bayanin wannan haramcin ya fito ne daga shalkwatan Rundunar ta ‘yan sanda dauke da sanya hanun Kakakinta DSP Kamal Datti Abubakar wanda ya rabar wa manema labaru a shekaran jiya, yana mai shaida cewar sun dauki kwararan matakai na kawo karshen tashin hankali musamman na ‘yan sara da suka a fadin jihar.
Ga abun da sanarwar tasu ke cewa, “A bisa bayyana cewar zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar a ranar 09/03/2019 wanda hukumar zabe ta ce zaben bai kammalu ba, inda ta ma sake cewar za a je zagaye na biyu a ranar 23/03/2019 a wasu sassan jihar. Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi tana kira ga jama’an jihar da su kasance masu bin doka da kauce wa karya dukkanin wata doka musamman a irin wannan yanayin da muke ciki na mawuyacin hali.
“Sannan kuma, a bisa rahotonnin wasu hare-haren ‘yan sara suka da suke kaiwa kan jama’a wanda mafiya yawa suna faruwa ne a sakamakon gangamin siyasa a cikin kwaryar garin Bauchi, rundunarmu ta baiwa jama’a tabbacin cewar za ta kawo karshen wannan matsalar, domn kuwa dukkanin matakai mun dauka cikin kwanciyar hankali da kyakkyawar matakai,” A cewar Rundunar.
Sun kara da cewa, “A bisa aikinmu na kare rayuka da dukiyar jama’a, Rundunarmu ta haramta dukkanin wani gangami ko zanga-zangar a fadin jihar Bauchi muddin babu izini. daga yau, dukkanin zanga-zanga ko gangami sai an samu amincewa kafin a gudanar da shi,” Inji Kakakin ‘yan sandan.
Sanarwar ta Datti ta nemi hadin kan jama’an jihar kan wannan matakin, suna masu shaida cewar sun dauki matakin ne kawai domin tabbatar da zaman lafiyar jihar da kuma kare rayuka da dukiyar jama’an jihar hadi da kawo karshen ‘yan bangar siyasa masu tayar da hankulan jama’a a jihar.
Wakilinmu dai ya shaida mana cewar tun bayan rashin bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi ake samun gungun matasa daban-daban suna gudanar da zanga-zangar a fadin jihar inda wasu ke neman a bayyana sakamakon zaben a yayin da wasu kuma suke bukatar a je zango na biyu na zaben, an samu rahotonnin tashin hankula a wasu sassan unguwannin jihar da kuma aikace-aikacen ‘yan daban siyasa wanda hakan ya jefa jama’a cikin zullumi.

Exit mobile version