'Yan Sanda Sun Kaddamar Da Cibiyar Yin Rijistar Motoci Ta Na'urar Zamani A Kebbi
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan sanda Sun Kaddamar Da Cibiyar Yin Rijistar Motoci Ta Na’urar Zamani A Kebbi

byUmar Faruk
2 years ago
'Yan sanda

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kebbi ta kaddamar da ofishin rajistar motoci ta na’urar zamani (CMR) domin yaki da masu aikata miyagun laifukan satar abin hawa.

Bukatar yin rajistar motocin na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘Yan sandan Jihar Kebbi, SP Nafi’u Abubakar, inda aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi.

  • Farashin Kayan Abinci Ya Ƙaru A Jihohin Nijeriya 36, Abuja, Kano, Borno Farashin Kaya Ya Sauka
  • Gidauniyar M-TECH Ta Tallafawa Yara Mabukata 400 Da Tallafin Karatu A Jihar Kebbi

Kazalika takardar ta kara da cewa, “A bisa shirin babban sufeton ‘Yan sanda na 22, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, NPM, Ph.D, na inganta harkokin tsaro a cikin gida Nijeriya, rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta bayar da umarnin kaddamar da babban ofishin yin rigistar motocin ta na’urar zamani wato ‘Digitalized Central Motor vehicle Registry (CMR)’ da ke Hedikwatar Rundunar a Gwadangaji, da ke a Birnin Kebbi.

Haka kuma ta kara ta cewa an yi shi ne don magance laifukan da suka shafi abubuwan hawa da nufin inganta lafiyar jama’a da tsaron mutanen jihar Kebbi.

Takardar ta ci gaba da cewa, duba da yadda manyan laifukan da suka shafi motoci ke karuwa, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sake farfado da babban ofishin rajistar motoci ta hanyar sanya shi a cikin na’ura mai kwakwalwa ta yadda za a rika amfani da bayanan mota guda domin ya ba da hakikanin bayanai daga ’yansandan a yayin gudanar da bincike na zamani wajen kokawa da laifukan satar motoci a fadin jahohin kasar nan.

Har ilayau, kaddamar da ofishin rajista yana da fa’idodi masu yawa, waɗanda suka haɗa da; inganta tsaro da samun bayanai na kai-tsaye daga na’urar CMR ga ‘yan ƙasa, haka kuma za su iya samun babban kwarin gwiwa ga tsaron motocinsu.

Haka kuma ingantattun bayanan abin hawa za su taimaka wajen dakile wa da magance laifuka satar motoci cikin sauki, da nufin tabbatar da cewa, an kiyaye kadarorin ‘yan kasa.

Hakazalika, ‘Yan sandan za su kasance mafi kyawun kayan aiki don aiwatar da dokokin da suka shafi motoci, kamar rajista da lasisi. Hakan zai haifar da samar da ingantattun hanyoyi da inganta hanyoyin tafiyar da ababen hawa da za su amfanar da duk masu amfani da ababen hawansu a kan hanya.

Bugu da kari takardar ta ce cikakkun bayanai na motoci za su zama abin hana masu aikata laifuka waɗanda za su iya amfani da ababen hawa don ayyukan da ba su dace ba. Sanin cewa jami’an tsaro na da damar samun ingantattun bayanai na iya hana aikata laifukan satar motoci a jahohin kasar nan.

Don haka Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi, CP Chris Aimionowane, psc, mnips, ya bukaci al’ummar Jihar masu son zaman lafiya da su rungumi shirin na IGP na kawo sauyi ta hanyar yiwa motocinsu rajistar ta na’uran zamani da nufin bayar da gudunmawarsu tare da inganta tsaro na cikin gida da tabbatar da tsaro ga kowa da kowa.

Daga karshe don yin rijistar motar ku, ku ziyarci https://cmris.npf.gov.ng ko tuntuɓi Jami’in da ke kula da ofishin yin rigiata a rundunar ‘yansanda ta jihar akan wannan Lamba 08062118443 ko don neman karin bayani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Next Post
Gwamna Dikko Zai Sake Tsarin Babbar Kasuwar Jihar Katsina

Gwamna Dikko Zai Sake Tsarin Babbar Kasuwar Jihar Katsina

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version