Sagir Abubakar" />

’Yan Sanda Sun Kama Katsinawan Da Ake Zargi Da Aikata Damfara

Damfara

Rundunar ’Yan Sandan Jahar Katsina ta kama wasu da ake zargin ’yan damfara ne da suka fito daga jahar Katsina.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai daga jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Gambo Isah.

Wakilinmu na fannin shari’a ya bamu labarin cewa wadanda aake zargin Kabiru Bashir da Sadik Ashiru daga karamar hukumar Danbattar jahar Kano sun kware wajen damfara ta hanyar kiran waya da sunan su aljannu ne.

Kamar yadda rahoton ya nuna, wadanda ake zargin sun sace wani katim ATM mallakar wata mai suna Rabi’atu garba yar karamar hukumar Mani ta jahar Katsina, inda suka kirata ta waya suna nuna cewa su aljannu ne tare da tambayar ta lambar katin cirar kudi (ATM), inda suka kwashe mata kudi Naira Miliyan daya daga asusun ajiyarta na banki.

Daukar kudin ya ja hankalinta, inda ta garzaya zuwa caji ofis na Katsina ta sanar masu batun, wanda suka gaggauta kama wadanda ake zargin.

Yayin da jami’an yan sandan ke bincikar wadanda ake zargin sun tabbatar wa  da hukumar cewa sun aikata laifin da ake zarginsu ga mutane da yawa a cikin jaharr Katsina.

Haka kuma jami’an ‘yan sanda sun kwace mota guda, tare da katin shedar aiki na hukumar tsaro ta farin kaya (Cibil Defense) da katin cirar kudi (ATM) guda biyu, da wayar hannu guda hudu 4 da kuma kimanin tsabar kudi Naira Dubu Dari da Ashirin daga hannun yan damfarar.

A halin da ake ciki dai har yanzu jami’an ‘yan sandan na cigaba da binciken al’amarin.

Exit mobile version