‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Tara Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Sakkwato

‘Yan sandan jihar Sakkwato sun bayyana cewa; sun kame mutum akalla tara wadanda ake zargi da garkuwa da jama’a da kuma fyade. Mutum bakwai daga cikinsu ana zarginsu da garkuwa da jama’a ne. A yayin biyu daga cikinsu ake zarginsu da aikata fyade.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Ibrahim Kaoje, ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa sun kama wadanda ake zargi ne an wurare daban-daban na jihar.

Kaoje ya ce; an kama Isiya Zubairu, mai shekara daga karamar hukumar Illela bisa zargin yiwa yarinya mai shekara shida fyade a cikin gidansu. Ya ce mutum biyu kuma ana zarginsu da yin garkuwa da mahaifinsu da ‘yarsa a Kauyen Rakaka Magaji dake karamar hukumar Rabah.

Ya tabbatar da cewa; atisayen Puff Adder ne tare da taimakon ‘yan sa kai suka yi nasarar cafke mutum shida da ake zargi inda aka yi nasarar kwatar abin hawa a hannunsu.

Ya ci gaba da cewa; Maude Salihu daga kauyen Yankara a jihar Katsina an kama shi ne a karamar hukumar Binji. An kama Salihu ne da kudi har naira dubu 417, 030, wayoyi biyu, da layin waya guda hudu, da kayayyakin tsafe-tafe. Inda ya tabbatar da cewa yana daga cikin wadanda suka addabi jihohin Katsina, Zamfara da Sakkwato. Inda ya ce bayan biyan wani kudin fansa ne aka ba shi na shi rabon.

Shi ko Bashiru Abdullahi, an kama shi ne a kauyen Dankade a karamar hukumar Rabah.

 

Exit mobile version