‘Yan Sanda Sun Kama Soja Da Tulin Tabar Wiwi A Jigawa

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta bayyana kama wani kofur din soja da daurin tabar wiwi 169, a Karamar Hukumar Ringim. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Jigawa, Bala Sanchi ne ya bayyana hakan da kan shi a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, yau Laraba.

Sojan dai kamar yadda Sanchi ya bayyana, an tura shi ne domin yaki da Boko Haram, amma ya tsere tun watanni bakwai da suka gabata. Kwamishinan ‘yan sanda Sanchi ya yi bayanin cewa an kama wanda ake zargin ne tun a ranar 17 Ga Satumba, wajen karfe 2:30 na rana. A cewar shi ‘yan sandan ‘Operation Puff Adder’ ne suka damke shi a kan titin Sankara zuwa Amaguwa, cikin Karamar Hukumar Ringim.

An kama shi ne a cikin mota kirar Toyota Camry, mai lamba KTU 833 DK. An kama shi bayan da jami’an ‘yan sanda suka samu labarin wani hatsari da motar ta yi.

“Yayin da suka isa wurin da motar ta yi hatsari, sun samu motar da ta yi hatsarin, mai lamba KTU 833 DK, samfurin Toyota Camry. Da suka yi tambaya, sai suka samu labarin cewa wani jami’in soja ne mai sanye da kakin soja ya tuko motar. Da jami’an mu suka tsananta bincike a cikin motar, sai suka samu daurin tabar wiwi har 169.” inji Sanchi

Ya kara da cewa; Wanda suka kama din a cikin kayan sojoji, kofur ne mai suna Muzambilu Abdullahi, da aka tura yaki da Boko Haram, amma ya gudu tun watanni bakwai da suka gabata. Da aka tsananta binciken sojan, ya ce wani mai suna Alhaji Abubakar daga Lokoja ne ya dauko shi, domin ya yi masa rakiya zuwa Maigatari, a Jihar Jigawa.

Da aka tambaye shi inda Alhajin ya ke, sai sojan ya ce ya gudu bayan da motar ta yi hatsari. Kwamishinan ‘yan sanda ya kara da cewa an kuma kama wasu mutane kusa da motar, wadanda bayan bincike suka tabbatar da cewa su ne dillalan da ke sayen tabar wiwi din da aka kama.

Exit mobile version