Yusuf Shuaibu" />

‘Yan Sanda Sun Kama Wasu ‘Yan Fashi A Jihar Legas

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legas ta cafke gungun ‘yan fashi mutum bakwai wadanda suka addabi mazauna Jihar Legas wajen yi masu fashi a ranar ‘Balentine.’
An bayyana cewa ‘yan fashin sun addabi mazauna titin College cikin garin Fagba da kuma yankin Abattoir da ke Jihar. Wadanda ake zargin dai su ne Lekan Akinyemi dan shekara 23, Chimeze Ofulie dan shekara 18, Babangida Abdullahi dan shekara 22, Abubakar Umaru dan shekara 30, Samuel Oyinloye dan shekara 24, Timileyin Oladipupo dan shekara 27 da kuma Habeeb Olayinka, an samu nasarar cafke su ne da misalin karfe 9 na dare a kan titin College cikin Ifako-Ijaiye ta Jihar Legas, bayan da gungun ‘yan fashin suka gama yi wa fasinjoji fashi da wuka da kuma sauran muyagun makamai.
A cikin bayanin da rundutar ta gabatar ranar Lahadi, ta bayyana cewa duka wadanda ake zargin sun fito ne daga sassa daban-daban na cikin kasar nan, amma suna zama ne a garin Abattoir da ke Agege ta Jihar Legas.
Wadanda ake zargin su yi wa Augustine Agafe fashi bayan ya sauka daga tasi a titin College da ke Ifako-Ijaiye. A cikin abin da suka amsa daga wajen wannan mutumin dai sun hada da wayar kirar ‘Android’ da kudi naira 14,000 da kuma jakar hannu.
Agafe ya bayyana cewa, “Sun yi min fashi ne saboda suna da yawa kuma suna rige da muyagun makamai, amma na yi kokarin bin sawun su lokacin da na bayyana wa mutane. Na bayyana wa jami’an tsaro da ke gudanar da sintiri a yankin, sun cafke wasu daga cikin su.
“Haka ma suka yi wa wasu mutane fashi ciki har da budurwa tare da saurayinta. ‘Yan fashin sun kwace musu wayoyinsu sannan suka caka wa saurayin wuka, domin yaki ya ba su wayan shi tare da walat din sa.”
A cikin bayaninsa, daya daga cikin gungun ‘yan fashin ya bayyana cewa sun yi wa fasinjoji fashi cikin dare, inda suka kwace musu wayoyinsu, jakunkuna, sarkuna da kuma walat.
Binciken ‘yan sanda dai ya bayyana cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Oladipupo wanda ake yi wa lakabi da ‘Timi Yahoo’, ya kware wajen satar waya tare da yin damfara a intanet wajen sata a asusun ijiya na mutane.
“Ina amfani da layin wayar da Akinyemi da kuma wasu kungiya a Agege suka bani wajen kara fadada hanyoyin fashin da muke yi a intanet wajen satar kudaden mutane a susun ijiya na mutane,” in ji Oladipupo.
Kwamishinan Jihar Legas Mu’azu Zubairu, ya bayar da umurnin cafke sauran ‘yan kungiyar, sannan ya bayar da umurnin mika lamarin ga sashin rundunar da ke yaki da masu fashi da makami domin gudanar da cikakken bincike. Ya kara da cewa, za a mika lamarin zuwa kotu da zarar an aka kammala bincike.

Exit mobile version