Khalid Idris Doya" />

‘Yan Sanda Sun Kame Wani Makashi A Enugu

Wani mutum da aka yi zargin ya hallaka wasu mutane uku ya fada komar ‘yan sanda a jihar Enugu.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar ta Enugu SP Ebere Amaraizu shine ya tabbatar da cafke wanda ake zargi da kisan mutanen, kana kuma wanda aka ayyana nemansa ruwa a jallo wato Chibuike Odoh, ‘yan sandan sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwar manema labaru da suka raba a Enugu.
Chibuike Odoh, wanda ya fito daga kauyen Mgbuji Ehamufu da ke karamar hukumar Isi-Uzo a jihar, ya kashe mutane daga wannan yankin nasa.
Amaraizu ya bayyana cewar wanda suke zargin an samu nasarar kamesa ne a ranar Juma’a daga rundunarsu masu aikin kota fado na sashin kwararru.
Ya ce, sun iya gano cewar Odoh’s yana aikata mummunar ta’asar tasar ne da wasu abokan cin burminsa masu suna Emmanuel Ani daga Amede Ehamufu.
Inda ya bayyana cewar a yanzu haka Odoh na ci gaba da taimaka wa rundunarsu domin samun nasarar gudanar da cikakken bincike kan masu irin wannan aika-aikar a fadin jihar domin taso keyarsu.
Kakakin ‘yan sandan ya tunatar kan dan ta’addan da suka sake kamewan, “Shi wannan da muke zargin, kwanan nan ya fito daga gidan yari a sakamakon laifukan da ya tafka a yankin Ehamufu, inda kuma bayan sako shi, yanzu haka ya sake kashe wasu akalla mutane uku da muke zarginsa da kashewa da kuma illata wani mutum guda,” In ji shi.

Exit mobile version