’Yan Sanda Sun Kashe Matasa Uku A Wurin Jana’iza A Jihar Ribas

A jiya ne ‘yan sanda su ka harbe wasu matasa guda uku, a yayin wata arangama tsakanin matasa da kuma ‘yan sanda a yankin Nkpolu da ke cikin karamar hukumar Obio/Akpor ta Jihar Ribas, lokacin da a ke gudanar da jana’iza waani matasa a yankin. An dai bayyana cewa, matashin da a ke yi masa jana’iza dai shi ne, Aleruchi Woko, ana zargin cewa, wani soja ne ya harbe matashin lokacin da matasa ke gudanar da zanga-zanga a shekarar da ta gabata.  A wurin jana’izan na jiya, an bayyana cewa, lamarin ya juya zuwa zab da jini, sa’ilin da ‘yan sanda su ka farmaki matasan lokacin da su ke dawowa daga wajen dauko gawar. An dai labarta cewa, ‘yan sanda su na da wata manufa, inda su ka mamaye wurin jana’izan tare da bude wa matasan wuta.

Matasa daga yankin sun bayyana cewa, ‘yan sanda cikin inifom sun tsare wasu matasa a yankin Obiri-Ikwerre cikin garin Rumuosi a karamar hukumar Obio/Akpor, lokacin da su ke kan hanyarsu ta zuwa dauko gawar mani matashi. Sun kara da cewa, matasan sun ki tsayawa, inda ‘yan sandar su ka bude musu wuta, nan ta ke su ka kashe mutum uku.

Lokacin da a ka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Ribas, DSP Nnamdi Omoni, ya bayyana cewa, ‘yan sanda sun samu bayanan sirri a kan ‘yan ta’adda wadanda su ba asalin ‘yan yankin ba ne, sun mamaye wurin Jana’izan. Omoni ya musanta cewa, an kashe mutune a yankin. Ya kara da cewa, an dai samu arangama tsakanin ‘yan sanda da kuma wasu matasa da a ka yi hayan su, amma dai babu wanda ya rasa ransa.

Exit mobile version