Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta samu nasarar kubutar da mutum goma sha biyar daga hannun masu garkuwa a karamar hukumar Chikun, da ke jihar Kaduna, kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan ya bayyana.
Aruwan ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ya rabawa manema labarai jiya Juma’a, a Kaduna. Aruwan ya ce, rundunar ‘yan sandan ta tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna cewa ta samu nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su din.
“Rundunar ‘yan sandan sun yi wa dajin da aka ajiye mutanen dirar mikiya, wanda ke karamar hukumar Chikun, wanda kuma a nan ne suka kwato wadanda aka yi garkuwar da su, kamar yadda ya ce.
Aruwan ya ce, bayan kuma wata musayar wuta da aka yi da masu garkuwar an sake kubutar da wasu mata guda uku a Rijiya Uku da ke yankin.
Matan da aka kubutar guda uku an yi garkuwa da su ne tun a cikin watan Nuwamba 18, 2020 lokacin da masu garkuwa suka yi wa kauyensu dirar mikiya suka yi awon gaba da su.
”Tun daga wancan lokacin suke hannun masu garkuwar, har zuwa wannan loaci da Allah ya kawo karshen lamarin. Aruwan, ya ci gaba da cewa, rundunar ‘yan sandan ta dada samun karfin gwiwa na kara fadada ayyukanta don ganin cewa an ceto dukkan wanda ya fada hannun masu garkuwar .
A kaeshe gwamna Nasir El-Rufai ya yabawa rundunar jami’an tsaron da suka yi wannan aiki, sannan kuma ya kara tabbatar musu da goyon bayan gwamnati don ganin sun samu nasara.