‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutum 8 Daga Gawurtattun Masu Satar Mutane A Kaduna

Rundunar ‘yan sandar Jihar kaduna, ta bayyana cewa ta yi nasarar kama wasu gawurtattun masu yin garkuwa da mutane, wanda a dalilin hakan ya kai su ga ceto wasu mutane takwas cikinsu har da wani yaro Dan shekara 13.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kakakin Rundunar ‘yan sandar Jihar kaduna, ASP Yakubu Sabo,  cikin wata sanarwa da ya fitar kuma aka raba ma manema labarai a kaduna.

Ya kara da bayyana cewa, jami’ansu sun sami nasarar kai sama manne a ranakun Talata da Alhamis, wanda a cewarsa, da sun sami wannan gagarumin nasarar ne da taimakon wani Kasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Mustafa Ibrahim.

ASP Sabo, ya ci gaba da bayyana cewa, an yi nasarar kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su ne a Yankin Rigasa da Narayi da ke kananan hukumomin Igabi da kuma Chikun, na Jihar kaduna.

Kakakin Rundunan ‘yan sandan Jihar Kadunan, ya kara da cewa, sai da suka dauki lokaci mai tsawo suna musayar wuta tsakaninsu da ‘yan ta’addan, a mafakarsu da ke cikin dajin Maguzawa da Gurguzu, kamin daga bisani suka yi nasarar kama wasu daga cikin ‘yan ta’addan, a yayin da wasu daga cikin su suka tsere da raunuka a jikinsu.

Sanarwar ta kara da cewa, ranar talata da misalin karfe 8 na dare, hadakar jami’an tsaro daga Rigasa da Nariya, da kuma hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda daga hedikwata, sun yi nasarar kama mai mai garkuwa da mutane mai suna Mustafa Ibrahim, a yankin Daura rod da ke Rigasa, a inda aka same shi da yin garkuwa da wani yaro dan kimanin shekaru 13, wanda ya yi garkuwa da shi daga Marabar Rido, da ke karamar hukumar Chikun, da niyyar daukanshi zuwa wajen sauran gungun masu garkuwa da mutanen da ke cikin daji a boye. Wanda a dalilin hakan ne jami’ansu suka yi nasarar kubutar da wasu mutum biyu, masu suna, Ismail Hussaini da kuma Husaini Umar, dukkaninsu mazauna layin Ado-Gwaram a Rigasa.

Wadanda aka yi nasarar kubutarwar sun hada da; Sada Abdullahi, Maimuna Umar Sharif, Husaina Umar Sharif, dukkaninsu mazauna Nariya ne da ke karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna, a cewarsa.

Exit mobile version