Jami’an yan sanda sun kulle hedikwatar uwar jam’iyyar APC bisa umurnin Sufeto-Janar na hukumar yan sanda, IGP Mohammed Adamu.
Hakazalika an samu labarin cewa Sufeto-Janar din zai gana da bangarorin kwamitin gudanarwan jam’iyyar a hedikwatar hukumar misalin karfe 1 na rana.
An tattaro cewa kwamishanan ‘yan sanda birnin tarayya ya umurci babban jami’in tsaron hedikwatar ya bayyanawa mambobin kwamitin gudanarwan jam’iyyar cewa babu wanda aka amince ya shiga hedikwatar.