Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta musanta labarin da ke cewa, an kai hari ofishin ‘yansanda da ke garin Shinkafi.
In za a iya tunawa, a ranar Alhamis din da ta gabata ce, aka samu rahoton cewa, ‘yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yansanda, inda aka kwashi bindigogi da harsasai.
Jin yadda wannan labari ya yadu, rundunar ‘yansanda ta jihar Zamfara, ta fitar da wata sanarwa wadda jami’in hulda da jama’a na rundunar,SP Mohammed Shehu ya sa wa hannu, ya ce, rahoton da aka bayar a jaridar Daily Trust a shafi na 8, ta ranar Asabar 25, ga watan Satumba, 2021, ba gaskiya ba ne, domin babu wani kai hari da aka yi a ofishin ‘yansanda da ke Shinkafi ta jihar Zamfara.
Haka kuma, rahoton kai harin Shinkafi ba gaskiya ba ne. Gaskiyar abin da ya faru shi ne, ranar Juma’a da safe, ‘yanbindiga nasu yawa sun yi yunkurin kai hari Shinkafi, amma sai hadin gwiwar jami’an tsaro da aka jibge a garin ya hana su iya kawo wannan harin.
“Babu wani rahoto na kashe wani jami’in tsaro ko kuma ‘yanbindiga. Haka kuma babu wani rahoto da ke nuna cewa, ‘yanbindigar sun tafi da wasu,”
Kamar yadda ya ce, akwai cikakken tsaro a garin na Shinkafi,al’umma na cigaba da kasuwancinsu. Sannan kuma ana cigaba da daukar sabbin matakan tsaro wadanda za su taimaka wajen tabbatar da samun dorewar zaman lafiya a wannan yanki.
Ya ce, al’ummar wannan yanki sun yi mamakin yadda jaridar ta Daily Trust ta bayar da wannan labara, ba tare da jin ta bakin jam’an ‘yansanda ko jama’ar gari ba.