Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Sanda Sun Sake Yin Artabu Da Masu Satar Mutane A Edo

by
1 year ago
in LABARAI
2 min read
legas
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo ta yi artabu da masu satar mutane, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da kubutar da mutane bakwai da aka sace, in ji wani jami’i.

Kontongs Bello, mai magana da yawun ‘yan sanda na Edo, ya fadi haka a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Labarai Masu Nasaba

Kungiyar Agaji Ta Kasar Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 131 Ga Marayu A Kebbi

Nijeriya Na Bukatar Shugaban Da Kasar Ce Kawai A Gabansa —Obasanjo

Ya ce, ‘yan sanda sun yi aiki tare da tawagar ‘yan banga na yankin don cimma nasarar.

Ya ci gaba da cewa, jami’an tsaron sun ci karo da wadanda ake zargin masu garkuwar ne a layin Ahor da ke hanyar Benin zuwa Lagos sannan suka yi artabu da su, inda aka kashe uku daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa ne. Amma bai ambata ko ‘yan sanda sun samu rauni ba a yakin.

Bello ya ce, tare da mutane bakwai da aka ceto, da kuma 13 da aka ceto a ranar Asabar da ta gabata, jimillar wadanda abin ya shafa tsakanin Asabar da Litinin sun kai 20 yanzu.

Wannan lamari na baya-bayan nan ya faru ne kimanin makonni biyu bayan da ‘yan sanda Edo suka yi wata arangama da wasu masu satar mutane a yayin musayar wuta a yayin da aka ceto mutane biyu da aka sace.

Wani jami’in ya ce, ‘yan sanda sun kuma gano kimanin Naira 200,000 daga hannun masu garkuwar a yayin lamarin na ranar 28 ga Afrilu.

Edo na daya daga cikin jihohin Nijeriya inda satar mutane don neman kudin fansa ta yi kamari. Sauran jihohin sun hada da Enugu, Kaduna, Katsina da Akwa Ibom.

A ranar Litinin, Bello ya bayyana cewa, sabuwar nasarar ita ce ci gaba da aikin gandun daji wanda Phillip Ogbadu, kwamishinan ‘yan sanda a Edo ya yi alkawarin.

Bello ya sake nanata cewa kwamishinan ‘yan sanda ya yi alkawarin ci gaba da wannan aiki kuma ba zai hakura ba har sai jihar ta kawar da masu satar mutane.

Ya ce, Ogbadu ya kuma nemi hadin kai da kawancen masu ruwa da tsaki ta hanyar musayar bayanai, musamman daga wadanda ke kusa da garin Ahor da kewaye.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Ramadan: Kara Imani Da Allah Shi Ne Mafita – Imam Abubilat Lokoja

Next Post

Rikicin Kalifancin Tijjaniyya Ya Sake Kunno Kai A Nijeriya

Labarai Masu Nasaba

Kungiyar Agaji Ta Kasar Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 131 Ga Marayu A Kebbi

Kungiyar Agaji Ta Kasar Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 131 Ga Marayu A Kebbi

by Umar Faruk
10 hours ago
0

...

Nijeriya Na Bukatar Shugaban Da Kasar Ce Kawai A Gabansa —Obasanjo

Nijeriya Na Bukatar Shugaban Da Kasar Ce Kawai A Gabansa —Obasanjo

by
12 hours ago
0

...

Legas: Mazauna Yankin Lekki Na Zaman Dar-Dar Kan Yuwuwar Kai Masu Hari

Legas: Mazauna Yankin Lekki Na Zaman Dar-Dar Kan Yuwuwar Kai Masu Hari

by Abubakar Abba
14 hours ago
0

...

2023: Kwamishinonin Ganduje 7 Da Ya Amince Da Ajiye Aikinsu Da Ukun Da Ya Yi Watsi Da Su

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Kwaleji 4 A Kaduna Sun Bukaci Kudin Fansa

by Abubakar Abba
15 hours ago
0

...

Next Post
Rikicin Kalifancin Tijjaniyya Ya Sake Kunno Kai A Nijeriya

Rikicin Kalifancin Tijjaniyya Ya Sake Kunno Kai A Nijeriya

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: