Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Sha Alwashin Dakile Bangar Siyasa A Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, ta sake nanata aniyarta na raba Jihar da duk wani nau’in ‘yan bangan siyasa kafin nan da babban zabe na 2019.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Malam Rabi’u Yusuf, ne ya bayyana hakan a wajen wani taron da ya yi da shugabannin Jam’iyyun siyasa na Jihar.

Kwamishinan wanda mataimakin sa mai lura da ayyuka, DCP Balarabe Sule, ya wakilce shi, ya karfafa cewa, “Lokutan da ‘yan siyasa za su rika tayar da hankulan al’umma ba tare da an hukunta su ba sun shude,” ya tabbatar masu da cewa rundunar ‘yan sandan ta shirya yin maganin duk wani dan siyasa da ke daukan nauyin ‘yan bangan da ke haddasa fitina a kowane sashi na Jihar.

Ya bukaci shugabannin Jam’iyyun da su hana ‘yan takaran na su yin siyasa tare da gaba, ya kara da cewa, ai siyasa ba abu ne na ko a mutu, ko a yi rai ba.

“Duk wasu tashin hankula da suke faruwa, ‘yan siyasa ne ke haddasa su, su suke ba matasa ‘yan bangan kwaya da makamai domin su tayar da hankali a lokutan zabe, suke yin hayar su domin su kai ma abokanan hamayyar su hari, amma a wannan karon muna son a canza daga wannan salon siyasar.

“A shirye muke mu bayar da tsaro a duk wani taro na siyasa ga kowace Jam’iyya, amma ba za mu raga ma duk wani dan siyasan da ya karya ka’idar abin ba. Duk wanda muka kama da kwaya ko makami a wajen taron siyasa za mu hukunta shi da kuma wanda ya dauki nauyin sa.

Ya kuma bukaci ‘yan siyasan da su baiwa Kwamishinan ‘yan sanada sanarwa a saura awanni 48 da su gudanar da duk wani taron siyasa domin su samar masu da tsaron da ya dace.

Shugabannin Jam’iyyun da suka halarci taron sun yaba, tare da alkawarin tsayuwa da ka’idojin da aka shimfida masu, domin samun gudanar da zaben na 2019 lami lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: