’Yan sanda sun tabbatar da kisan dan uwan Akanta Janar na Jihar Imo da masu garkuwa da mutane suka yi.
Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Imo ta tabbatar da kisan kani ga Akanta Janar na Jihar Imo, Mista Balentine, wanda aka fi sani da Obiezu. Obiezu, wanda attajiri ne kuma babban ma’aikaci a kamfanin mai. An ruwaito cewa masu garkuwa da mutane sun kashe shi, yayin da suka yi kokarin yin garkuwa da shi kauyensu kuma basu samu nasara ba, Akatta da ke yankin Oru ta Gabas a jihar.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, Obiezu ya koma gida ne domin bikin sabuwar shekara lokacin da lamarin ya faru. Amma, wasu majiyoyi daga kauyen sun ce Obiezu yana tuka motarsa ne kirar Toyota Hilud a kan titin Orlu-Mgbidi a lokacin da masu garkuwar suka tare shi.
“Ba su ma jira shi ba ya tsaya ya sauko daga motarsa ba a lokacin da suka bude wa motar wuta. Masu garkuwar sun turo shi daga cikin motar sannan suka tafi da ita ”, kamar yadda wani mazaunin kauyen ya shaida wa wakilinmu.
“Ina so in yi kira ga gwamnatin jihar, ‘yan sanda da sauran hukumomi da cibiyoyin da abin ya shafa da su hanzarta tunkarar kalubalen kafin ya tabarbare zuwa matakin da zai gagari duk wata mafita a cikin dogon lokaci.”